170524-Ziyarar-aikin-da-yan-jaridun-CRI-suka-kammala-a-lardin-Hebei.m4a
|
A yayin wannan ziyara, 'yan jardiun sun ziyarci birane da dama na wannan lardin, wadanda suka hada da birnin Shijiazhuang, da Cang Zhou, da Xianghe, Langfang. Bugu da kari a yayin wannan ziyara, tawagar 'yan jaridun, ta ziyarci wurare da dama masu muhimmanci a lardin da suka hada da kamfanin harhada magungunan gargajiya da na zamani na Yiling, da kamfanin samar da na'urorin wutar lantarki mai zaman kansa na Kelin dukkansu a birnin Shijiazhuang.
Sauran wuraren da tawagar 'yan jaridun ta ziyarta sun hada da kamfanin madara na Junlebao, da kamfanin samar da makamashi mai tsafta na ENN da rumbun adana bayanai mai suna Range Data centre, da tashar jiragen ruwa da sabon yankin raya tattalin arziki na Bohai da kuma rukunin kamfanonin mutum-mutumin inji dake Xianghe.
Wannnan ziyara ta baiwa tawagar damar ganin irin ci gaban da lardin na Hebei ya samu da irin rawar da wadannan kamfanoni ke takawa a fannonin kimiyya da inganta lafiyar bil-Adam da tattalin arzikin da harkar kasuwanci tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. Haka kuma ziyarar ta kara nuna wa tagawar tarin albarkatun dake lardin Hebei. (Saminu/Ibrahim/Sanisu Chen)