in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana babban taro game da Somali a matsayin babbar nasara
2017-05-12 13:08:03 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana babban taron da aka gudanar a London game da Somalia a matsayin taro mai cike da nasara.

Taron wanda ya kunshi kasar Birtaniya, da Somalia, da MDD, da kungiyar tarayyar Afrika, kuma ya samu halar abokan hulda 42 dake kasar Somalia.

Shugaban kasar Somali Mohamed Abdullahi Farmaajo shi ne ya jagoranci tawagar kasar.

Takardar bayan taron ta bayyana cewa yanzu an samu wata dama ta tsara wata ajanda don farfado da kasar Somali wanda yake samun tallafin alummar kasashen duniya nan da shekaru 4 masu zuwa da kuma na dogon zango.

Sai dai takardar bayan taron ya nuna cewa har yanzu ayyukan ta'addanci na yin barazana ga zaman lafiya da sha'anin tsaron kasar inda ake bukatar samar da tsarin mulki da zai kara nazarin hanyoyin da zasu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Batun cigaba sha'anin tsaro a kasar baya tafiya cikin sauri kamar yadda aka tsara sannan ga yawaitar ayyukan masu fashin teku.

Sanarwar ta kara da cewa ana bukatar Karin cigaba a fannonin cigaban demokaradiyya, da 'yancin dan adam, da fannin tsara dokoki, da yaki da rashawa, da rage talauci da bunkasuwar tattalin arziki. Matsalar yunwa na daga cikin muhimman abubuwan dake bukatar daukin gaggawa a kasar.

Gwamnatin Somali da kasashen duniya a shirye suke su yi aiki tare game da wadannan batutuwa uku – karfafa tsaron kasa da tabbatar da tsaron kasa da kasa, ingantuwar sha'anin siyasa da farfado da cigaban tattalin arziki, kamar yadda takardar bayan taron ta ambata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China