in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar 'yan jarida na CRI zuwa lardin Shaanxi
2017-05-17 13:38:23 cri

A ranar 23 zuwa 29 ga watan Afrilun shekarar 2017 ne hukumar gudanarwar gidan radiyon kasar Sin CRI tare da hadin gwiwar hukumar gudanarwa ta lardin Shaanxi suka shirya wata muhimmiyar ziyarar aiki ga yan jaridu zuwa lardin Shaanxi, wanda ya kunshi 'yan jaridu wadanda ke aiki a gidan rediyon kasar Sin CRI da suka hada da yan jaridun kasashen waje dake aiki a CRI daga kasashe sama da 20, da suka hada da Faransa, Japan, Singapore, Thailand, Malasiya, Masar, Turkiyya, Uruguay, Laos, Najeriya, Indiya, Kenya, Koriya ta kudu da sauransu, kana tawagar ta hada da wasu 'yan jaridun gwamnatin tsakiya, da na lardin Shaanxi, sun ziyarci birane da dama da suka hada da birnin Xi'an, Baoji, Xianyang, Jinyang dake lardin na Shaanxi, a yayin ziyarar, tawagar yan jaridun, sun ziyarci wuraren da dama masu muhimmanci a lardin da suka hada da wuraren adana kayan tarihi, da raya al'adu, da wasu masana'antu da sauran wurare da suka samu bunkasuwa cikin sauri a sassa daban daban. Haka kuma, kamfanin intanet wato CRI Online da ofishin kula da harkokin watsa labarai na lardin Shaanxi ne suka shirya wannan ziyara ta hanyar yin hadin gwiwa. Tawagar yan jaridun sun zagaya muhimman wurare masu yawa don ganemwa idonsu tare da gudanar da tambayayi ga hukumomin da abin ya shafa. (Ahmad/Ibrahim/Sunusi)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China