Wani gwajin lissafi da aka yi ya shaida cewa, sabuwar na'urar lissafin tana da saurin da ya dara na sauran na'urorin da aka yi gwajinsu a sauran kasashen duniya sauri har a kalla sau dubu 24.
Pan Jianwei ya kara da cewa, wannan sabuwar na'urar da aka kera ta shaida ci gaban da kasar Sin ta samu a wannan fanni, lamarin da ya aza harsashi mai inganci ga tabbatar da kwarewar harkar lissafi da za ta zarce na gargajiya. (Lubabatu)