in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala ziyarar 'yan jaridun CRI a lardin Shanxi
2017-05-03 10:53:53 cri

A ranar 29 ga watan Afrilu ne aka kammala ziyarar aiki a lardin Shanxi na 'yan jaridu wadanda ke aiki a gidan rediyon kasar Sin CRI da suka hada da 'yan jaridun kasashen waje dake aiki a CRI daga kasashe kimanin 20, da wasu 'yan jaridun gwamnatin tsakiya, da na lardin Shanxi, sun ziyarci birane da dama na wannan lardin, wadanda suka hada da birnin Xi'an, Xianyang da kuma Baoji, a yayin ziyarar, tawagar 'yan jaridun, sun ziyarci wuraren da dama masu muhimmanci a lardin da suka hada da wuraren adana kayan tarihi, da raya al'adu, da wasu masana'antu da sauran wurare da suka samu bunkasuwa cikin sauri a sassa daban daban na biranin Xi'an da Xianyan da kuma Baoji dake lardin na Shanxi.

Haka kuma, ofishin kula da harkokin watsa labarai kan shafin intanet na lardin Shanxi da ofishin kula da harkokin watsa labarai ga ketare na lardin Shanxi da CRI Online na Gidan Rediyon CRI ne suka shirya wannan ziyara ta hanyar yin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China