170501-Shaanin-yawon-shakatawa-a-gidajen-manoma-da-matan-birnin-Kudus-suke-gudanarwa-Bilkisu.m4a
|
A duk lokacin da ambaci birnin Kudus, yawancin mutane suna daukar wannan ne a matsayin wuri mai tsarki da mabiyan addinin Yahudawa, addinin Kirista da kuma addinin Musulunci ke taruwa don harkokin Ibada. Amma, ban da batun da ya shafi addinai, sha'anin yawon shakatawa a gidajen manoma da matan wurin suke gudanar, shi ma ya jawo hankulan al'umomin kasashe daban daban. Saboda wasu mazauna wurin sun fito ne daga kasashe da kabilu daban daban na Turai, Afirka da kuma Gabas ta tsakiya da dai sauransu, don haka gidajen manoma a wurin yana kunshe da halin musamman na abubuwa da dama ta fannin sha'anin yawon shakatawa, inda masu yawon shakatawa suke iya dandana abincin manoma iri daban daban, ban da wannan kuma a kan nishadantar da su ta fannonin wake-wake da kide-kide, da zane-zane da dai sauransu, har ma su kan yi cudanya kwarai tare da masu aikin fasaha. Amma, abin da ya fi ba mu sha'awa shi ne, yadda kirkirar ta fito daga sha'anin yawon shakatawa a layi na Beijing na kasar Sin.