Wannan gari ya jima yana huldar cinikayyar ganyen shayin Fu da kasahen dake kan hanyar siliki.
An gano fasahar sarrafa ganyen shayin Fu a kamfanin sarrafa ganyen shayi na Jingyang tun a shekarar 1068 wato shekaru 949 da suka gabata.
Wannan yanki yana matukar jan hankalin al'umma daga sassa daban daban na kasar Sin da ma kasashen ketare wadanda suke zuwa yankin don yawon bude ido.
Yankin shine mafi shahara wajen sarrafa ganyen shayin Fu a yammacin kasar Sin, wanda ke da matukar dadin sha da kara lafiya a jikin bil adama, har ma ya iya rage kiba.(Murtala Zhang)