170426-Ranar-Littafi-da-kare-yancin-mallakar-fasaha-ta-duniya.m4a
|
Ranar littafi da kare 'yancin mallakar fasaha ta duniya ta samo asali ne tun a shekarar 1616 lokacin da aka yi rashin wasu fitattun marubuta irinsu Cervants, da Sharkspare da Inca Garcilaso de La vega. Kana a shekarar ce kuma aka samu wanzuwar wasu fitattun marubuta kamar Maurice Droun da Haldor K Laxness, da Vladimir Nabokov, da Josep Pla da Manuel Mejia Vallejo da sauransu.
A ranar 23 ga watan Afrilun shekarar 1995 ne babban taron kungiyar kula da harkokin Ilimi, kimiya da al'adu ta MDD wato UNESCO yayin babban taronta ta nuna girmamawa ga muhimmancin litattafa da kuma marubuta, a wani mataki na karfafawa jama'a gwiwa musamman matasa game da muhimmancin karatu da kuma girmama wadanda suka ba da gudummawa ga harkokin rubuce-rubuce.
Tun lokacin da aka fara ayyana wannan rana, abokan hulda suke bikin wannan rana, lamarin da ya nuna muhimmancin watsa labarai ko amfani da littafi a rayuwar bil-Adama.
Bayanai na nuna cewa, miliyoyin jama'a daga kasashe sama da 100 ne suke murnar wannan rana ciki har da daruruwan kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da kungiyoyin kwararru da 'yan kasuwa masu zaman kansu.
A iya tsawon wannan lokaci, wannan rana ta littafi da 'yancin kare mallakar fasaha ta duniya da ake bikinta a ranar 23 ga watan Afrilun kowa ce shekara, ta janyo hankulan jama'a daga nahiyoyi da bangarorin rayuwa daban-daban game da muhimmancin litattafi da kare 'yancin mallakar fasaha.
Sai dai duk da muhimmancin wannan jigo, har yanzu akwai wasu rukunin matasa a wannan zamani da ba sa karanta litattafai, Hakan a cewar masu sharhi, ba ya rasa nasaba da wanzuwar kafofin sadarwa na zamani.
Masu fashin baki na cewa,akwai bukatar matasa su kara mayar da hankali ga harkar rubuce-rubuce da kuma karanta litattafai, a wani mataki da kare tarin gudummawar da marubutu ke bayarwa ga ci gaban rayuwar dan-Adam daga dukkan fannoni.(Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)