A saboda haka kasar ta bukaci kasashen Koriya ta kudu da Amurka da su janye na'urorin kana su dakatar da jigilar ragowar wadannan na'urori.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba, ya kuma bayyana cewa, girke na'urorin babu abin da zai haifar illa kara dagula al'amura a yankin, tare da kara tsanta halin da ake ciki a zirin koriya. Kuma hakan ba zai taimaka a kokarin da ake na kawar da makaman nukiliya a zirin ba, baya ga kara kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Ibrahim)