in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a iya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa amfani da tsarin kudaden musaya na SDR
2017-04-22 12:48:30 cri
Mr. Yi Gang, mataimakin gwamnan babban bankin kasar Sin wato Bankin al'ummar kasar Sin PBOC, ya ce bankin zai iya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa amfani da tsarin kudaden musaya na SDR.

Yi Gang ya bayyana haka ne a yayin taron da asusun bada lamuni na duniya IMF da bankin duniya suka shirya, inda ya ce tun bayan da takardar kudin kasar Sin wato Renminbi ta shiga cikin masu amfani da tsarin SDR, amfani da shi a matsayin mizanin awon hada-hadar kudi da asusun ajiya ya samu tagomashi.

A cewar mataimakin gwamnan, kasar Sin ta fara ajiya da adana bayanan hada-hadar kudin da tsarin SDR, kuma bankin duniya da bankin Standard Chartered sun yi nasarar ba kasar takardar lamunin bisa tsarin SDR.

Sai dai, Yi ya ce akwai bukatar inganta tsarin saboda bai tanadi tsarin cinikayyar kadarori da ruwan kudi ba tare da asara ba, sannan kuma har yanzu farashin zuba jari ya yi tsada.

A don haka, ya ba da shawara ga cibiyoyin kasuwanci da su inganta amfani da SDR a matsayin mizanin awon asusun ajiya wanda zai karfafawa kasuwar cinikayyar kadarori da kudade. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China