Sakataren ma'aikatar lafiya na Kenya Cleopa Mailu ne ya bayyana haka, yayin wani taron karawa juna sani kan yaki da cutukan lokacin zafi da ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya da hadin gwiwar hukumar samar da magungunan gargajiya na kasar Sin da kuma jami'ar nazarin magungunan gargajiya ta Guangzhou suka shirya.
A jawabinsa yayin bude taron, Cleopa Mailu ya yabawa kasar Sin bisa gudunmawar da take bayarwa wajen yaki da cutar malaria da ke sanadin rayukan yara da mata masu juna biyu a Afrika.
Ya kara da cewa, suna jinjinawa masana kimiyya na kasar Sin da suka gano sinadaran hada maganin Artemisinin, wanda ya zo a lokacin da maganin cutar malaria ke kokarin zama kalubale ga duniya.
Ya kuma bayyana cewa, ingantattun masana'antun samar da magunguna na kasar Sin sun ba kasashen Afrika kwarin gwiwar samar da magunguna da kansu tare da inganta hanyoyin tunkarar cutukan kokacin zafi masu kisa.
Har ila yau, Cleopa ya ce a shirye kasashen Afrika suke, su yi amfani da magungunan gargajiya na kasar Sin wajen yakar cutar malaria da aka dorawa alhakin asarar kaso 1.5 na tattalin arzikin kasashen da cutar ta fi kamari. (Fa'iza Mustapha)