in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata a rubu'in farko
2017-04-14 12:44:46 cri

Kakakin kwamitin yi wa tattalin arziki kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, a rubu'in farko na bana, tattalin arzikin kasar ya samu tagomashi.

A jiya ne kakakin kwamitin yi wa tattalin arziki kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin Yan Pengcheng ya bayyana cewa, kamar yadda aka samu ci gaban tattalin arziki tun bayan watan Yunin shekarar da ta gabata, kasar Sin ta na ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki a rubu'i na farko na bana, wato watanni uku na farkon shekarar da muke ciki, kana ana gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin kasar bisa shirin da aka tsara.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki a fannin samar da kayayyaki, kuma an samu ci gaba a bayyane, a saboda haka, al'ummar kasar sun himmantu wajen kafa sabbin kamfanoni ta hanyar yin kirkire kirkire.

Haka zalika hukumomin gwamnatin kasar, na kokarin tunkarar haduran da za a iya fuskanta. Ban da haka kuma, tattalin arzikin kasashen duniya shi ma ya na farfadowa akai akai. Kakakin kwamitin Yan Pengcheng ya bayyana cewa, "An yi hasashen cewa, kasuwar kasar Sin za ta ci gaba da samun kyautatuwa, kamfanonin kasar Sin kuwa, za su kara zage damtse yayin da suke kokarin neman ci gaba, kana adadin guraben aikin yi a kasar zai karu. Ban da haka kuma, tsarin sana'o'in kasar zai ci gaba da ingantuwa,haka zalika, harkokin cinikayya da kasashen waje. Adadin ribar da aka samu wajen masana'antu da adadin kudin da gwamnatin kasar ta tattara domin gudanar da aikinta sun karu sosai."

Wasu alkaluman da aka samu sun nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin tana da inganci. Misali, a farkon watanni 3 na bana, adadin lantarkin da ake amfani da shi a fadin kasar ya kai kilowatt biliyan 1450 a kowace awa, adadin da ya karu da kaso 6.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Haka kuma, Adadin kayayyakin da aka yi jigilar da su ta jiragen kasa ya karu da kaso 15.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin wannan lokacin a bara. Alkaluman PMI wato farashin sayen kayayyaki na aikin samar da kayayyaki ya kai kaso 51.8 bisa dari, alkaluman da ya kai sama da kaso 51 bisa dari cikin watanni 6 da suka gabata a nan kasar Sin.

Game da makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, kakakin ya bayyana cewa, akwai matsaloli da dama da kasar Sin ke fuskanta yayin da take kokarin samun ci gaban tattalin arziki. Yan Pengcheng yana mai cewa,"A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba lami lafiya, kuma ana kokarin rage wasu kayayyakin masana'antun da ba a bukata, kana farashin wasu kayayyakin da ake bukatar su da yawa yana sauyawa, misali a makon farko na watan Afililun bana, farashin man fetur na kasashen duniya ya karu da kaso 6 bisa dari, saboda sauyawar yanayin da kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki."

Yan Pengcheng ya fayyace cewa, tun daga farkon shekarar 2016, aka fara gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki iri na kara zuba jari iri na masu zaman kansu a cikin kamfanonin gwamnati har sau biyu, kuma a yanzu bangarori masu zaman kansu za su iya zuba jari a kamfanonin gwamnati, inda a yanzu aka shiga mataki na uku na gudanar da shirin. Yan Pengcheng ya kara da cewa, "Kamfanoni 19 na gwamnatin da aka zaba domin gudanar da kwaskwarima wato su shigo da jari na masu zaman kansu sun hada da sana'o'i da dama, misali sayar da lantarki da kera na'urorin samar da lantarki, da jiragen kasa na zamani, da jigilar kayayyaki ta jiragen sama, da samar da hidimar bayanan sufurin jiragen sama, da sadarwa, da samar da kayayyakin tsaron kasa, da harkokin kudi da dai sauransu. A cikin su, kamfanonin dake da nasaba da aikin soja sun fi yawa, inda adadinsu ya kai bakwai. Nan gaba kuma za a fara gudanar da kwaskwarima kan tsarin dake shafar man fetur da kuma iskar gas."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China