Jama'a assalam alaikum. Daga ranar 14 zuwa 15 ga watan Mayun bana, za a gudanar da babban dandalin tattaunawa kan 'ziri daya da hanya daya' na kasashen duniya a nan birnin Beijing. Domin kara fadakar da jama'a kan wata muhimmiyar manufa ta kasar Sin, gidan rediyon kasar Sin CRI zai kaddamar da gasar wasa kwakwalwa kan ilmin harkokin "ziri daya da hanya daya" mai taken 'Na san hanyar siliki' daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayun bana.
Jama'a, za ku iya ganin tambayoyin a shafinmu na Intanet wato hausa.cri.cn, gami da shafinmu na sada zumunta na Facebook, wato CRI HAUSA.
Gidan rediyon CRI zai duba amsoshin da za ku turo mana, tare da zabar wadanda suka lashe gasar. Haka kuma duk wanda ya ci gasar, zai samu damar samun wasu kyaututtuka, ciki har da akwatin rediyo, da zanen yadin siliki na gargajiya na kasar Sin.
Za a tura amsoshin ne ta adireshinmu na Email wato hausa@cri.com.cn
Allah ya ba mai rabo sa'a.
Ga Tambayoyin:
1. An takaita "ziri daya da hanya daya" daga wace jimla?
A. "zirin tattalin arziki na hanyar siliki"
B. "hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21"
C. "sabuwar hanyar siliki"
2. Ta yadda ake furta kalmar "ziri daya da hanya daya"
A. A ran 7 ga watan Satumba na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin "zirin tattalin arziki na hanyar siliki" karo na farko, a yayin da yake gabatar da jawabi a jami'ar Nazarbayev dake kasar Kazakhstan.
B. A ran 3 ga watan Oktoba na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da burin gina "hanyar siliki ta ruwa ta karni na 21" cikin hadin gwiwa a yayin da yake gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar Indonesia.
3. Wadanne fannoni ne suka kasance masu muhimmanci ga hadin gwiwar shirin "ziri daya da hanya daya"?
A. tuntubar juna a kan manufofi
B. hada juna da hanyoyi
C. rashin saka shinge ta fannin cinikayya
D. yin amfani da tsabar kudi ta juna
E. mu'amala a tsakanin al'ummar kasashe daban daban
4. Wadanne ka'idoji ne kunshe cikin shirin raya "ziri daya hanya daya"?
A. yin shawarwari da juna
B. raya yankin tare
C. cin moriyar ci gaban yankin tare
5: Wadanne kasashe ne shirin bunkasa tattalin arziki na "ziri daya hanya daya" ya shafa?
A. Sin da Mongoliya da Rasha
B. Asiya da Turai
C. Sin-tsakiyar Asiya-yammacin Asiya
D. Sin-Yankin kudancin Asiya
E. Sin da Pakistan
F. Bangaladesh da Sin da Indiya da Myanmar