A daya hannun kuma, akwai kuma wasu jami'an Indiya dake furta kalaman da ba su dace ba dangane da batun kan iyakar. A game da wannan, a yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, tuni gwamnatin kasar Sin ta bayyana rashin jin dadin ta ga kasar Indiya, kuma za ta kara daukar matakai don kiyaye ikonta da tsaronta.
A gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, Lu Kang ya ce, wannan ziyarar da Dalai Lama ke yi, ta wuce abin da bangaren Indiya ke bayyanawa a matsayin aikin da ya shafi addini. Kuma matakin na Indiya ya saba wa alkawarin da gwamnatin kasar ta dauka game da batun Tibet, kuma zai haifar da illa ga shawarwarin da Sin da kuma Indiyan ke yi, a kokarin daidaita takkadama da ke tsakaninsu kan batun yankunansu. (Lubabatu)