in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 4 na Basic suna da niyyar ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris wajen tinkarar sauyin yanayin duniya
2017-04-12 10:50:31 cri

A ran 10 da na 11 ga wata a nan birnin Beijing, an yi taro karo na 24 na ministoci masu kula da sauyin yanayin duniya na kasashen Brazil da Afirka ta kudu da Indiya da Sin, wato kasashe 4 na Basic, inda ministoci suka tattauna kan matakan da ya kamata a dauka domin ci gaba da aiwatar da "yarjejeniyar Paris", har ma suka yi musayar ra'ayoyinsu kan jerin muhimman batutuwan dake shafar matakan da za su dauka kafin shekarar ta 2020, da matakan da kowacensu za ta dauka a cikin gida da yadda za a yi hadin gwiwa irin ta a zo a gani tsakanin kasashen 4. Daga karshe dai, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka nemi dukkan kasashe wadanda suka sa hannu kan "yarjejeniyar Paris" da su goyi bayan yarjejeniyar kamar yadda suka yi tun da farko domin moriyar bil Adama da al'ummomi masu zuwa a nan gaba.

Kasashe 4 na Basic, wani tsari ne da kasashen Sin da Indiya da Brazil da Afirka ta kudu, wato manyan kasashe masu tasowa suka kafa a shekarar ta 2009. Bayan kafuwarta, kasashen 4 sun taka muhimmiyar rawa wajen ingiza yin tattaunawa kan sauyin yanayin duniya, da tsaron hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da moriyarsu, har ma sun bayar da muhimmiyar gudunmmawa ga kokarin daddalewa da kuma aiwatar da "yarjejeniyar Paris".

A yayin taron manema labaru da aka shirya bayan taron, Mr. Xie Zhenhua, wakilin musamman wanda ke kula da harkokin tinkarar sauyin yanayin duniya a kasar Sin ya bayyana cewa, "Kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan tinkarar sauyin yanayin duniyarmu, kuma tabbas za ta sauke nauyin da aka dora mata. Kasar Sin ta riga ta gabatar da gudunmmawar da za ta bayar wajen tinkarar sauyin yanayin duniyarmu. A cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 13 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewarta, burin da za ta cimma a shekarar 2020 ya riga ya zama aikin dole da za'a kammala. Na amince da cewa, zuwa shekarar 2020, kasar Sin za ta cika alkawuran da ta dauka gaba daya."

A yayin wannan taron ministocin kasashe 4 na Basic, ministocin kasashen sun yi musaya da kuma daidaita ra'ayoyinsu kan yadda za a ingiza daukar matakan tinkarar sauyin yanayin duniyarmu tsakanin kasa da kasa gaba daya bisa halin da ake ciki a tsakaninsu wajen tinkarar sauyin yanayin duniya, musamman sun yi tattaunawa kan yadda za a karfafa matakan da za a dauka kafin shekarar 2020 da matakan da kasashensu za su dauka a gida da yadda za a yi hadin gwiwa irinta a zo a gani da sauran batutuwa. Ministocin sun nuna cewa, ya kamata kasashe masu arziki su cika alkawuran da suka dauka na samar da kudi da fasahohin zamani da makamantansu ga kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayin duniyarmu. Malama Barbara Thompson, mataimakiyar ministan kula da harkokin muhallin kasar Afirka ta kudu ta bayyana cewa, "Muna fatan kasashe masu arziki su cika alkawuransu na samarwa kasashe masu tasowa dalar Amurka biliyan 100 a kowace shekara. Yanzu mun gane cewa, a halin siyasa da ake ciki a kasashen duniya, 'yarjejeniyar Paris' sakamako ne mafi kyau da aka samu sakamakon kokarin kowane bangare. 'Yarjejeniyar Paris' ta samar da wani tsarin ka'ida daga dukkan fannoni da kuma samun daidaito tsakanin bangarori daban daban."

A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2015, bangarori kusan 200 wadanda suka kulla "Takardar ka'idodin tinkarar sauyin yanayin duniya" sun zartas da "yarjejeniyar Paris" a yayin taron Paris na tinkarar sauyin yanayin duniya, inda suka tsara shirin tinkarar sauyin yanayin duniya da za a yi bayan shekarar 2020. A karshen shekarar da muke ciki, za a yi taro karo na 23 na bangarori wadanda suka kulla "Takardar ka'idodin tinkarar sauyin yanayin duniya" a birnin Bonn na kasar Jamus. Wannan taro zai taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da matakai bisa "yarjejeniyar Paris". Saboda mai yiyuwa ne gwamnatin kasar Amurka za ta canja matsayinta kan batun tinkarar sauyin yanayin duniya, Mr. Xie Zhenhua, ya bayyana cewa, "Kafin a kaddamar da taron tattaunawar da za a yi a watan Mayu mai zuwa, ministocin kasashe 4 na Basic sun yi taro, sun fitar da wata alamar siyasa, wato dole ne mu tsaya tsayin daka kan matsayin ciyar da aikin gaba. Haka kuma, dole ne mu kasashe 4 mu cika alkawuranmu, za mu bayar da gudummawar da muka dauki alkawarin bayarwa. Mun kuma amince da cewa, sauran kasashen duniya ma za su cika alkawuransu yadda ya kamata." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China