Jiyar Talata ne Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da Netumbo Nandi-Ndaitwah, mataimakiyar firaministan kasar Namibiya kuma ministar harkokin wajen kasar wadda ke ziyarar aiki a birnin Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin.
A yayin ganawar, Wang Yi ya ce, kasar Sin na son zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninta da kasar ta Namibiya, da kara yin mu'amalar al'adu, da taimakawa juna a al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, a kokarin bunkasa huldar da ke tsakaninsu daga dukkan fannoni.
A nata bangaren, Netumbo Nandi-Ndaitwah ta ce, kasarta ta yi fatan kara cin gajiyar aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Ta kuma yi maraba da kamfanonin kasar Sin, ciki har da masu zaman kansu da su zuba jari da habaka cinikinsu a Namibiya, tare da shiga ayyukan raya kasa. (Tasallah Yuan)