in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin ya gana da mataimakiyar firaministan kasar Namibiya kuma ministar harkokin wajen kasar
2017-04-12 10:11:36 cri

Mamba a majalisar gudanwar kasar Sin Yang Jiechi, ya gana da Netumbo Nandi-Ndaitwah, mataimakiyar firaministan kasar Namibiya kuma ministar harkokin wajen kasar a nan Beijing.

Yayin ganawar a Jiya Talata, Yang Jiechi ya ce, kasar Sin ta na fatan kasashen 2 za su zurfafa hadin gwiwa, ta yadda za su mori juna a dukkan fannoni, da kara kawo wa jama'arsu alheri, bisa amincewar juna ta fuskar siyasa da dankon zumunci da ke tsakanin jama'a tare da taimakawa juna ta fuskar tattalin arziki.

A nata bangaren kuma, Netumbo Nandi-Ndaitwah ta ce, kasarta na yabawa kasar Sin, la'akari da taimakon da take bayarwa ba tare da son kai ba cikin tsawon lokaci.

Ta kara da cewa, Namibiya na son inganta hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen 2 a sassa daban daban bisa muradin samun nasara tare, tare da kara taimakawa juna a al'amuran kasa da kasa, a kokarin kiyaye hakkokin kasashe masu tasowa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China