Jihar Qinghai za ta zuba makuden kudade don kyautata hanyoyin sufuri na matsugunin 'yan kabilar Tibet
Hukumar kula da hanyoyin sufuri ta jihar Qinghai dake nan kasar Sin, ta ce a shekarar da ta gabata, jimillar kudin da aka zuba a fannin raya harkokin sufuri a jihar, sun kai kusan Yuan biliyan 39, yayin da a bana kuma, ake sa ran kara yawan jarin da za a zuba a wannan fanni.
An ce daga shekara ta 2016 zuwa ta 2020, adadin yawan kudin da za'a zuba a wannan fanni, zai wuce Yuan biliyan dari biyu. Kana zuwa karshen shekara ta 2020, harkokin sufuri a matsugunin 'yan kabilar Tibet dake jihar Qinghai zai kara kyautata ainun. (Murtala Zhang)