Ma'aikatan ceto sun ce, za su ci gaba da gudanar da aikin ceto zuwa gobe 10 ga wata.
Shugaban kasar Kolumbiya Juan Manuel Santos Calderon, ya isa birnin Mocoa jiya, inda ya tabbatar da cewa, za'a farfado da samar da wutar lantarki ga yankunan dake fama da bala'in cikin mako guda, kana nan da wata guda, za'a samar da wadataccen ruwa ga mutanen da bala'in ya shafa.(Murtala Zhang)