in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Amurka suna ganin cewa, ya kamata a samu hanyar da ta dace domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka
2017-04-07 10:53:34 cri

Jiya Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa jihar Florida domin ganawa a karon farko da takwaransa na Amurka Donald Trump, kwanakin baya ba da dadewa ba, wasu masanan kasar ta Amurka sun gaya wa wakilanmu cewa, ganawar da shugabannin kasashen biyu wato Sin da Amurka za su yi a tsakaninsu tana da babbar ma'ana, kana sun bayyana cewa, ya kamata sassan biyu su sanya kokari matuka domin neman samun wata hanyar da ta dace domin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.

Wannan ganawa karo na farko ne da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi tsakaninsu tun bayan da sabuwar gwamnatin kasar ta Amurka ta fara mulkinta, a saboda haka, ganawar za ta taka muhimmiyar rawa a fannonin kara dankon zumunci da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma karfafa tsaro da zaman lumana da samun bunkasuwa a yankin Asiya da tekun Pasific, dama duniya baki daya.

Daraktan cibiyar nazari kan harkokin gabashin Asiya ta jami'ar Johns Hopkins ta Amurka Kent Calder yana ganin cewa, huldar dake tsakanin Sin da Amurka za ta kawo babban tasiri ga tsarin siyasa da na tattalin arziki a fadin duniya, shi ya sa ganawar da shugabannin biyu za su yi ta jawo hankalin jama'a. Kent Calder yana mai cewa, "Ya kamata kasashen Sin da Amurka su yi kokari domin samun wata hanyar da ta dace domin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, saboda muna sa ran Sin da Amurka za su taka rawa domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata. A ganina, ganawar za ta samar da sakamako mai kyau, duk da cewa, ana damuwa kan huldar cinikayya dake tsakanin sassan biyu. Ana iya cewa, shugabannin biyu sun yi ganawa tsakaninsu ne a lokacin daya dace, saboda idan ba a gudanar da huldar dake tsakanin Sin da Amurka lami lafiya ba, to, lamarin zai kai yin illa ga harkokin kudi da cinikayya a duniya baki."

Har kullum ana mayar da huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka a matsayin abu mafi muhimmanci yayin da ake gudanar da huldar dake tsakanin sassan biyu. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka shekaru 38 da suka gabata, sai huldar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu ta samu yalwatuwa cikin sauri, bisa alkaluman da aka samar, an ce, a shekarar 2016, adadin cinikayyar kayayyaki tsakanin Sin da Amurka ya kai dalar Amurka biliyan 519 da miliyan 600, adadin da ya karu da ninki sama da 200 idan aka kwatanta da na shekarar 1979, lokacin da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin sassan biyu. Yanzu dai, kasar Sin ta riga ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar ta Amurka, haka kuma ta kasance kasuwa mafi girka ta uku da Amurka ta fitar da kayayyaki, a sa'i daya kuma, Amurka ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta biyu ta Sin, kana ta kasance kasuwa mafi girma da kasar Sin ke fitar da kayayyaki.

Shehun malamin jami'ar Harvard ta Amurka Dwight Perkins ya yi nuni da cewa, hakikanin yanayin da ake ciki ya bukaci Sin da Amurka su kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, saboda hakan ya dace da moriyar sassan biyu. Perkins yana ganin cewa, babu zabi a gaban Sin da Amurka, sai gudanar da hadin gwiwa. Yana mai cewa, "Yin gaba da juna yayin da ake yin cinikayya zai lahanta kowa da kowa, kuma hakan zai yi illa ga moriyar Amurka, saboda a halin da ake ciki yanzu, shugaba Trump yana kokarin raya tattalin arzikin Amurka, tare kuma da kara samar da guraben aikin yi, idan ana son cimma burin, ya fi kyau a gudanar da hadin gwiwa tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China