in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke tsohuwar shugabar kasar Koriya ta kudu bisa zargin aikata rashawa
2017-03-31 14:01:12 cri
Tsohuwar shugabar kasar Koriya ta kudu Park Geun-hye, an damke ta da safiyar yau Juma'a bayan wani umarni da kotu ta bayar, inda ake hasashen idan laifukan da ake zarginta da su na aikata rashawa suka tabbata, zata iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai.

Wani alkali a kotun tsakiyar birnin Seoul ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, babban laifin da ake son tabbatarwa shi ne yunkurin da ta yi na kokarin lalata duk wasu shedu da ake nema game da shara'ar da ake yi mata.

Takardar sammacin na Madam Park, masu gabatar da kara sun gabatar da ita ne a farkon wannan mako, bayan samun umarnin kotun a ranar Alhamis din data gabata, bayan wata shara'a da aka gudanar har ta tsawon sa'o'i 9 wanda kuma shine lokacin sauraron shara'a mafi yawa da aka taba samu a tarihin kasar.

Park tayi ta jiran sakamakon shara'ar da kotun ta gabatar har zuwa dare a ofishin mai gabatar da kara a tsakiyar Seoul.

Matar mai shekaru 65, ana tunanin tsare ta da aka yi ba lallai ne ya zama hukunci na karshe ba, amma akwai yiwuwa ta fuskanci hukuncin daurin rai da rai. Idan zargin cin hanci da ake mata ya tabbata zata sha dauri na shekaru 10 mafi karanci.

Ana saran Park, zata fara fuskantar hukuncin ne nan da karshen kwanaki 20 da zata yi a gidan kaso, saboda tuhumar da ake yi mata na aikata laifuka 13, ciki har da zargin aikata rashawa, da yin amfani da ikonta a lokacin tana shugabancin kasar, da kuma bayyana wasu bayanan sirrin gwamnati.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China