in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawar da shugabannin Sin da Amurka za su yi za ta kawo tasiri ga hulda tsakanin kasashen biyu
2017-03-31 10:53:14 cri

Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi ganawa da shugaba Trump a Mar-a-Lago dake jihar Florida ta kasar Amurka tsakanin ranekun 6 zuwa 7 ga wata. Shahararren kwararren mai yin nazari kan harkokin kasar Sin, kana darektan cibiyar yin nazari kan yanayin da kasar Sin ke ciki ta John L. Thornton ta kungiyar Brookings dake birnin Washington na Amurka Li Cheng ya yi nuni da cewa, ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi tana da muhimmanci kwarai, har za ta kawo babban tasiri ga huldar dake tsakanin sassan biyu a nan gaba.

Bayan da gwamnatin kasar Sin ta sanar da labari game da ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi, sai fadar White House ita ma ta bayar da wata sanarwa a safiyar ranar 30 ga watan Maris, inda ta bayyana cewa, shugabannin biyu wato Xi Jinping da Trump za su tattauna harkokin kasa da kasa da na shiyya shiyya da suke jawo hankalin sassan biyu, kana shugaba Trump da uwargidansa za su shirya liyafa a daren ranar 6 ga wata, domin yin maraba da zuwan shugaba Xi da uwargidansa.

A titin birnin Washington, wani mazaunin birnin ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da huldar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, yana mai cewa, "A fannin tattalin arziki, sassan biyu wato Sin da Amurka suna dogaro da juna, idan ba a shigo da kayayyaki kasarmu daga kasar Sin ba, to, za mu gamu da matsala, a sa'i daya kuma, kasar Sin ita ma tana bukatar yin hadin gwiwa da kasar ta Amurka."

Amma kwanakin baya ba dadewa ba, tsohon ministan kudi na Amurka Henry Paulson ya bayyana a yayin wani taron da aka gudanar a nan birnin Beijing da cewa, huldar dake tsakanin Sin da Amurka tana kara yamutsewa, a saboda haka kamata ya yi a gyara ta.

Darektan cibiyar yin nazari kan yanayin da kasar Sin ke ciki ta John L. Thornton ta Brookings Li Cheng yana ganin cewa, da gaske ne huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala a cikin 'yan shekarun da suka gabata, amma yanzu huldar ta kyautata, dalilin da ya sa haka shi ne domin hikimar da shugaban kasar Sin ya nuna yayin da yake daidaita matsalar. Li Cheng ya bayyana cewa, yanzu kasashen duniya suna fuskantar babban kalubale a fannoni da dama, shi ya sa wajibi ne manyan kasashe su kara hada kai domin tinkarar matsalolin dake gaban daukacin kasashe duniya, yana mai cewa, "Bai kamata ba manyan kasashe su mai da hankali kan moriyar kansu kawai, kamata ya yi su kara ba da muhimmanci kan kalubale a fannin tsaro da kasashen duniya ke fuskanta."

Li Cheng ya kara da cewa, kasashen Sin da Amurka manyan kasashe ne a duniya wadanda ke kawo babban tasiri ga yanayin da daukacin kasashen duniya ke ciki, shi ya sa ganawar da shugabannin kasashen nan biyu za su yi tana da babbar ma'ana, ana sa ran ganawar za ta kawo alheri ga al'ummomi a fadin duniya. Li Cheng ya yi hasashe cewa, yayin ganawar da za su yi, shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwa a fannoni uku, na farko shi ne tsaro, misali, yaki da ta'addanci, da hana yaduwar makaman nukiliya, ya nuna cewa, ba zai yiyu ba a kasa kula da mugun tasirin da gwajin makaman nukiliya na kasar Korea ta Arewa ke kawo mana, dole ne shugabannin biyu za su yi musanyar ra'ayi kan wannan kalubale mai tsanani dake gabanmu, kana sassan biyu za su tattauna kan huldar tattalin arziki da ciniki dake tsakaninsu. Li Cheng ya ci gaba da cewa, ban da duk wadannan hakikanan batutuwa, shugabannin biyu za su yi shawarwari kan tsarin yin cudanya dake tsakanin sassan biyu. Kafin wannan, tsare-tsaren cudanya tsakanin Sin da Amurka sun yi yawa, har adadinsu ya kai sama da 105, shi ya sa a nan gaba, za a rage wasu domin kaucewa rashin fahimta tsakaninsu.

Li Cheng ya yi nuni da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne ganawar da shugabannin biyu za su yi za ta kawo babban tasiri ga makomar huldar dake tsakanin kasashen biyu, saboda kila ne gwamnatin Trump za ta fara aiwatar sabuwar manufarta a yankin Asiya da tekun Pasifik, Li Cheng yana mai cewa, "Duk da cewa, ba mu ga sabuwar manufa ba tukuna, amma mun ga kokarin da gwamnatin Amurka ke yi, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya taba ambata manyan tsare-tsaren kasarsa a cikin shekaru 50 masu zuwa yayin da yake ziyara a nan Beijing, shi ma ya bayyana cewa, ya amince da manufar rashin nuna kiyayya da yin hargitsi, tare kuma da nunawa juna biyayya domin samun moriya tare da gwamnatin kasar Sin ta nace."

Li Cheng yana ganin cewa, ra'ayin Tillerson ya wakilci manufar da shugaba Trump zai aiwatar yayin da yake kokarin raya huldar dake tsakanin kasarsa da Sin, a saboda haka, ana iya cewa, ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi za ta kawo babban tasiri ga makomar huldar dake tsakanin sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China