in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
minista: Najeriya zata samar da ingantaccen tsarin amfani da albarkatun ruwa a kasar
2017-03-31 10:26:46 cri
Ministan albarkatun ruwa na Najeriya Suleiman Adamu, yace gwamnatin kasar ta kuduri aniyar aiwatar da wasu managartan hanyoyin amfani da albarkatun ruwa a kasar.

Ministan ya fadi hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron karawa juna sani mai taken "Tattaunawa ta kasa game da amfanin ruwa da aiwatar da dokokin ruwa na shekarar 2016" a Abuja, fadar mulkin kasar, Adamu yace gwamnatin Najeriyar zata fara aiwatar da dokoki da kuma bada lasisi ga masu hakar rijiyoyin birtsatse, har ma da duba yadda ake ta'ammali da ruwa a kasar ta hanyar amfani da hukumar nan ta kula da albarkatun ruwa ta kasa wato (NIWRMC) a takaice.

An dai kafa NIWRMC ne da nufin daidaita hakkokin da suka shafi yadda ake ta'ammali da albarkatun ruwa a kasar.

Ministan ya shedawa mahalarta taron cewa, ruwa daya ne daga cikin albarkatun kasar mafi muhimmanci wanda ke bukatar yin tattalinsa yadda ya kamata, ta hanyar aiwatar da dokoki da suka shafi tattalin arziki da dauwamamman cigaba.

Ya kara da cewa, amincewa da yin amfani da dokar samar da lasisin ta 2016, da kuma shirin samar da ruwa na kasa na 2016, wasu hanyoyoyin da zasu taimaka wajen tafiyar da al'amurran da suka shafi albarkatun ruwa yadda ya kamata.

Ministan yace aiwatar da dukkannin wadannan tsare tsare da suka hada da na tattalin arziki da zamantakewa a kasar da kuma yin amfani da masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da dokokin da samar da lasisin game da sha'anin tattalin albarkatun ruwa, wasu jerin gwanonin dabaru ne da zasu kara inganta fannin albarkatun ruwa a kasar baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China