in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Morocco da Sin sun amince da karfafa dangantaka ta fuskar daidaita harkokin cinikayya
2017-03-29 15:11:56 cri
Hukumar kula da takarar hajojin cinikayya ta Morocco da hukumar ciniki da masana'antu ta kasar Sin SAIC, sun amince da karfafa dangantaka ta fuskar daidaita harkokin cinikayya.

Wata sanarwa da hukumar kula da takarar hajojin cinikayya ta Morocco ta fitar jiya Talata, ta ce yayin wata ziyara a Rabat babban birnin Morocco, shugaban hukumar Abdelali Banamour da shugaban hukumar SAIC ta kasar Sin, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna game da musayar fasahohi da horas da jami'ai da nufin tsaftace harkokin cinikayya.

Ganawar da shugabanin hukumomin biyu suka yi, ya kuma bada damar tattauna batutuwan da suka shafi dokoki da ka'idojin kasa tsakanin kayayyaki na kasashen biyu, wanda ke da nufin bunkasa hadin giwa tsakaninsu.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Ministan cininki da masana'antu da zuba jari da harkokin tattalin arziki na zamani na kasar Morocco Moulay Hafid Elalamy, da shugaban Hukumar SAIC na kasar Sin Zhang Mao suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna kan inganta hadin gwiwarsu a bangaren kare 'yancin masu sayen kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China