in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kayayyakin da ake kai wa har gida ya zarce biliyan 30 a kasar Sin a bara
2017-03-29 14:32:42 cri

Hukumar kula da aikin gidan waya ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto kan ci gaban da aikin kai kayaki har gida na kasar ya samu a shekarar 2016, inda ya nuna cewa, aikin kai kaya har gida a kasar Sin, ya samu bunkasa cikin sauri, karon farko ke nan da yawan kayayyakin da ake kai wa har gida ya zarce biliyan 30.

Rahoton da hukumar ya fitar a Jiya Talata ya ce A halin yanzu, wannan adadi ya zama na farko a duk fadin duniya, wanda kuma ya zarce rubu'in na duniya baki daya, har ma yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar a fannin ci gaban sha'anin kai kaya har gida na duniya ya kai kashi 60 cikin dari.

Mizanin ci gaban aikin kai kaya har gida na kasar Sin, wani mizani ne da aka fara tantancewa daga shekarar 2010, kuma an sanya maki 100 a matsayin mizanin farko.

Mizanin ya kunshi fannoni hudu, wato girman aikin, ingancin hidima, habakar aikin, da kuma makomar aikin.

Bisa rahoton ci gaban aikin kai kaya har gida na kasar Sin na shekarar 2016 da hukumar kula da aikin gidan waya ta kasar ta fitar jiya, mizanin ci gaban aikin ya kai 538.5, wanda ya karu da kashi 40.8 cikin dari akan na shekarar 2015. A cikin mizanin, girman aikin ya fi jawo hankalin mutane. Geng Yan, wata jami'a ta hukumar kula da aikin gidan waya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shekarar 2016, mizanin aikin kai kaya har gida na kasar Sin ya kai 1104.6, wanda ya karu da kusan kashi 50 cikin dari bisa na shekarar 2015.

"karon farko, yawan kayayyakin da aka kai har gida ya zarce biliyan 30, a shekarar 2016, wanda ya karu da kashi 51.4 cikin dari akan na shekarar 2015. Lamarin da ya sa aikin kai kaya har gida ya ke zama ja gaba a cikin ayyukan hidima na kasar Sin, wanda kuma ya bada gudummuwa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Bugu da kari, girman aikin na kasar Sin ya zama na farko a duk duniya, adadin kuwa ya zarce rubu'in na duniya, har ma yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar a fannin ci gaban bangaren ya kai kashi 60 cikin dari."

Ban da wannan, mizanin ingancin hidima na aikin kai kaya har gida na kasar Sin ya samu karuwa a shekarar 2016. Madam Geng Yan ta furta cewa, an samu wannan kyautatuwa ne sakamakon ci gaban muhimman ayyukan yau da kullum na wannan bangaren.

"Kamfanonin kai kaya har gida na Shentong, Yuantong, Shunfeng, Yunda da ma Zhongtong sun fara sayar da hannayen jarinsu daya bayan daya, hakan ya tattara makudan kudade don raya muhimman ayyukan yau da kullum na kamfanonin. Yanzu ana gina manyan cibiyoyin rarraba kayaki a wasu muhimman wurare, kuma yawan sabbin cibiyoyin da aka fara amfani da su ya kai 20. Bugu da kari, ana ta kyautata tsarin sufuri ta jiragen sama. Inda kawo yanzu, yawan jiragen sama dake aiki na musamman na kai kayaki har gida ya kai 81. Haka zalika, aikin sufuri ta layin dogo mai matukar sauri ya jawo hankalin mutane, inda yawan kayayyakin da aka yi sufurinsu ta layin dogo mai matukar sauri a yayin bikin sayayya na watan Nuwambar bara ya zarce miliyan 15.25, wanda ya bude wani sabon shafi na hadin gwiwa tsakanin aikin kai kaya har gida da aikin sufuri ta layin dogo mai matukar sauri."

Ban da samun karuwa a fannonin girman aikin kai kaya har gida da kuma ingancin hidima, an kuma gabatar da bukatar kai kaya har gidan da ke yankunan karkara a cikin babban shiri na farko gwamnatin kasar Sin na shekarar 2016, hakan ya kara azama ga kamfanonin kai kaya har gida wajen daukar matakan kai kaya zuwa yankunan karkara. Madam Geng Yan ta bayyana cewa,

"sakamakon ci gaban aikin kai kaya har gida a yammacin kasar Sin da ma yankunan karkara da hukumar kula da ayyukan gidan waya ta kasar ta dukufa a kai, da ma aikin hadin gwiwa tare da masu sayarwa a kan Intanet na kauyuka, ya zuwa karshen shekarar 2016, aikin kai kaya har gida ya shafi kauyuka da garuruwa da yawansu ya zarce kashi 80 cikin dari. A birnin Shang Hai, da lardin Jiangsu da ma sauran larduna shida, aikin ya shafi dukkan kauyuka da garuruwa."

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, yawan kayayyakin da za a kai har gida a kasar Sin zai kai biliyan 42.3 a bana, adadin da zai karu da kashi 35 cikin dari akan na bara. Yayin da Yawan kudin shiga da za a samu daga aikin, zai kai Yuan biliyan 516.5, wanda zai karu da kashi 30 cikin dari bisa na bara.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China