in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Tashin hankali ya haifar da nakasu wajen shirin yaki da yunwa a kusa da gabashi da arewacin Afrika
2017-03-28 09:43:04 cri
Sabon rahoton da MDD ta fitar ya nuna cewa, matsalar karanci abin da rashin abinci mai gina jiki a kusa da gabashi da arewacin Afrika ya sake ta'azzara a shekaru biyar din da suka gabata, kuma matsalar ta kara kamari ne kafin a samu raguwar matsalolin rashin abinci mai gina jiki da rashin wadataccen jini, da talauci a shekarar 2010, kamar yadda mai magana da yawun MDD ya shedwa 'yan jaridu a jiya Litinin.

Farhan Haq, mataimakin kakakin MDD ya fadawa taron manema labarai cewa, tabarbarewar al'amurran da ake fuskanta, ya faru ne a sanadiyyar karuwar tashe tashen hankula, kana ya bayyana rahoton wanda shirin hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta bayyana game da matsalar karancin abincin dake addabar gabashi da kuma arewacin Afrika.

Haq, ya ce, baya ga matsalolin tashe tashen hankula da suka addaba yankunan, rahoton ya kuma tabo batun karancin ruwan sha, da sauyin yanayi a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin da suka kawo nakasu ga shirin yaki da yunwa, da samar da abinci da inganta abinci mai gina jiki wanda MDD ta kudiri aniyar cimmawa nan da shekarar 2030.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China