Lam Cheng Yuet-ngor ta yi nasarar lashe zabe karo na biyar wanda aka gudanar a yau a matsayin babbar jami'a mai kula HKSAR.
Kakakin hukumar ya ce an gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali, kuma zaben ya cika dukkan ka'idojin da hukumar gudanarwa ta HKSAR ta gindaya, wanda ya yi daidai da matakin da kwamitin gudanarwa na majalisar dokokin kasar Sin ya tanada. Da kuma dokokin na HKSAR, wanda ya kunshi yin zabe a bayyane, mai adalci da kuma gaskiya.
Bugu da kari, ofishin tuntuba na gwamnatin tsakiya a yankin Hong Kong mai cin gashin kai, HKSAR ya taya Lam Cheng Yuet-ngor murnar lashe zaben da aka yi karo na biyar a Hong Kong a yau Lahadi. (Ahmad Fagam)