in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana son tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya
2017-03-25 17:38:58 cri

A yau Asabar ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin nahiyar Asiya a garin Boao dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.

Cikin jawabinsa mai taken "hada hannu wajen tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya, don samar da kyakkyawar makoma ga tattalin arzikin nahiyar Asiya da ma daukacin duniya", mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli ya ce, ci gaban Asiya na bukatar samun goyon baya daga sauran sassan duniya, sannan samun walwala a duniya na bukatar ciyar da tattalin arzikin nahiyar Asiya gaba.

Yayin taron na dandalin tattalin arzikin nahiyar Asiya na Boao, Mataimakin firaministan kasar Sin Mista Zhang Gaoli, ya bayyana cewa,

"kasashen nahiyar Asiya sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya, kuma sun ciyar da tattalin arzikin kasashensu gaba cikin sauri, lamarin da ya ba mutanen duniya mamaki. Haka zalika, kasashen Asiya sun bada gudunmuwa wajen samun karuwar tattalin arzikin duniya.'

A cewarsa, kamata ya yi, kasashen su yi la'akari da yanayin da duniya ke ciki, da kokarin dacewa da manufofin zamani, da ci gaba da dogaro da fasahohin da aka samu, sannan su hada gwiwa wajen tabbatar da dunkulewar tattalin arziki da ciniki cikin 'yanci.

Ban da haka kuma, jami'in ya ce a watan Janairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wani muhimmin jawabi a wajen taron dandalin tattalin arzikin duniya na Davos, inda ya yi bayani mai zurfi kan batun dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. Zhang Gaoli yana mai cewa,

"Bayanin shugaba Xi Jinping ya nuna mana hanyar da ya kamata a bi, don tunkatar matsalolin tattalin arziki da duniya ke fuskanta, da inganta walwalar al'umma."

Mataimakin firaministan kasar Sin ya kara da cewa, don cimma burin da aka sanya gaba, ya kamata a tsaya kan manufar neman samun ci gaba cikin zaman lafiya, da kwanciyar hankali. Sannan a kara kirkiro sabbin fasahohi, da gyare-gyaren manufofin gwamnati, ta yadda za a iya kafa wani sabon tsarin tattalin arzikin duniya.

A cewar jami'in na kasar Sin, sauran ayyukan da ya kamata a yi sun hada da kara bude kofa ga 'yan kasuwa, da kuma bada dama ga dukkan bangarori don amfana da manufar dunkulewar tattalin arzikin duniya, gami da tabbatar da adalci a tsakanin al'ummomin.

Har ila yau, Mataimakin firaministan kasar Sin ya kara da cewa, wannan shekarar tana da matukar muhimmanci, ganin yadda jam'iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin za ta gudanar da wani babban taro, kuma za a ci gaba da zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar Sin wajen daidaita tsarin da ake bi na samar da kayayyaki.

Ya ce a wannan lokaci ne kuma, kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da samun karuwar tattalin arziki, da daidaita manufofin kasar, da kara inganta walwalar al'umma, gami da kokarin magance fuskantar hadari a bangaren tattalin arziki, ya na mai cewa, ta haka ne, za a samu damar tabbatar da kwanciyar hankali a kasar a dukkan fannonin tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

Ban da haka kuma, jami'in ya ce kasar Sin za ta kara bude kofarta ga karin 'yan kasuwan kasashen waje, kuma za ta ba su matsayi irin daya da masu masana'antu na kasar Sin, da nufin samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da kara janyo hankali masu zuba jari daga kasashen ketare.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China