in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton UNDP: An mayar da miliyoyin mutane saniyar ware a duniya
2017-03-22 10:44:56 cri
Rahoton shirin cigaban kasashe na MDD UNDP ya fitar a jiya Talata, ya nuna cewa, akwai miliyoyin mutane a duniya wadanda aka mayar da su saniyar ware daga amfana daga duk wani nau'in cigaba, kuma hakan zai iya kara tsananta muddin dai ba a daidaita matsalar nuna musu kyama da banbanci, da rashin basu damar shiga a dama dasu a harkokin siyasa.

Rahoton mai taken "Cigaban dan adam na kowa da kowa" UNDP ta fitar da shi a jiya Talata a Stockholm.

UNDP tace, game da batun cigaban bil adama a cikin shekaru 25, akwai mutane masu dubun yawa wadanda har yanzu basu samu cigaba na azo a gani ba, sakamakon irin shingen dake tsakaninsu da samun cigaban.

A cewar rahoton akwai bukatar a mayar da hankali wajen daukar matakai na gaggawa don kawar da duk wani shinge dake zama barazana ta dakile cigaban rayuwar bil adama.

Rahoton yace koda yake an samu cigaba ta fuskar yanayin rayuwar dan adam a dukkan sassan duniya tsakanin shekarar 1990 zuwa 2015, sai dai har yanzu guda daga cikin mutane 3 yana rayuwa ne kasa da matakin cigaban bil adama, kamar yadda alkaluman kididdigar cigaban dan adam suka nuna.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China