in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron dandalin tattauna harkokin bunkasuwar kasar Sin ya mai da hankali kan dunkulewar duniya
2017-03-21 13:21:53 cri

A jiya Litinin, aka rufe taron shekara shekara na dandalin tattauna harkokin bunkasuwar kasar Sin wanda majalisar gudanarwar kasar Sin ta gudanar. Taron na tsawon yini biyu ya mai da hankali ne kan dunkulewar duniya, kuma mahalarta taron suna ganin cewa, kasashen duniya baki daya suna cin gajiyar dunkulewar duniya, kuma aikin da za a sanya a gaba shi ne a duba yadda kasa da kasa za su ci moriyar dunkulewar tare. Dan gane da batun, Lubabatu na tare da karin haske.

A yayin da ake kara fuskantar rashin tabbas ta bangaren ci gaban tattalin arzikin duniya, dunkulewar duniya ya kara jawo hankalin mutanen duniya da ke dukufa kan harkokin siyasa da tattalin arziki. Don haka, a gun taron shekara shekara na dandalin tattaunawar harkokin ci gaban kasar Sin na shekarar 2017, shugaban bankin zuba jari kan manyan ayyukan Asiya, Mr.Jin Liqun ya bayyana cewa, kasashen duniya baki daya na cin gajiyar dunkulewar duniya, ya ce, "kasashen duniya baki daya na cin gajiyar dunkulewar duniya, duk da cewa mun bambanta da juna ta fuskar saurin bunkasuwa, amma ban amince da ra'ayin cewa akwai kasashen da ba su amfana ba. In dai har an tsaya a kan ra'ayin, lalle manufar cikin gida na kasashen ne bata dace ba, kamata ya yi a daidaita manufar. Ban da haka, abin lura shi ne, kasashe maso tasowa da suka amfana daga dunkulewar duniya sun kware wajen tsara manufofin cikin gida da ma aiwatar da su, sa'an nan kuma, kasashe masu tasowa da dama da suka ci moriyar, su ma suna karkashin tsarin duniyarmu da kasashe masu ci gaba ke jagoranta."

A ganin Mr.Jin Liqun, duniyarmu za ta kasance cikin cin moriyar juna da kuma ingantuwar tsarin kulawa da harkokin duniya a wannan karni na 21 da muke ciki, don haka ana bukatar dunkulewar duniya. Sai dai hakan ba ya nufin kowace kasa za ta amfana daga ciki, ya zama dole su yi kwaskwarima a gida. A ganin jami'in, dalilin da ya sa aka fuskanci wasu matsaloli shi ne yadda kasa da kasa suka bambanta da juna ta fannin cin moriyar dunkulewar. Ya kara da cewa, "An fuskanci wasu matsaloli ta fannin dunkulewar duniya da ma dunkulewar tattalin arzikin duniya, dalili kuwa shi ne bambanci mai yawa da kasa da kasa suke fuskanta ta fannin cin moriyar dunkulewar, abin da kuma ya fi jawo damuwar al'umma, musamman ma kasashen da ba su amfana sosai daga dunkulewar ba da ma jama'arsu."

A gun taron kuma, tsohon sakataren kudi na kasar Amurka, Jacob J.Lew ya yarda da ra'ayin na Mr.Jin Liqun, kuma ya ce, bambancin manufofin cikin gida da kasashen duniya suke da su shi ya sa kasashen ba su kai ga cin moriyar dunkulewar duniya yadda ya kamata ba. A ganinsa, ya kamata a duba yadda za a sa dunkulewar duniya ta samu karin karbuwa daga kasashen duniya. Jami'in ya ce, "A gun taron G20 ko kuma tarurrukan irin wannan, bai dace ba mu masu tsara manufofi mu yi bayani kawai a kan dalilin da ya sa ake fuskantar wadannan matsaloli masu wuya, a maimakon haka, ya kamata mu bayyana wa al'umma wadanne sauye-sauye ne manufofin za su iya kawo wa zaman rayuwarsu, da ma sauye-sauyen da za su faru ga bangaren samar da guraben aikin yi. A cikin gida kuma, ya kamata mu yi kokari mu duba shin yaya za a kara cin moriyar dunkulewar duniya. Idan za a kara cin moriyar, ta yiwu za mu tabbatarwa al'umma dunkulewar duniya abu ne mai kyau, kuma idan kowa zai iya cin moriyar, lalle za a iya kara tabbatar musu cewa, dunkulewar tana samar da riba."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China