in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar 'yar jarida ta Nijeriya a kasar Sin
2017-03-17 15:04:26 cri

A ranar 1 ga watan nan na Maris ne aka bude taro na 4, na ilmantar da 'yan jaridun nahiyar Afirka, game da muhimman batutuwa da suka shafi kasar Sin, da ma yanayin da ake ciki game da alakar kasar da nahiyar Afirka, a wani mataki na fadada musaya tsakanin Sin da nahiyar ta Afirka ta fannin watsa labarai. Kaza lika taron zai baiwa 'yan jaridu daga nahiyar ta Afirka damar ganewa idanun su, irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin siyasa, da raya al'adu da kuma inganta rayuwar al'umma da dai sauran sassan na ci gaba, a shirin da aka yiwa lakabi da CAPC.

Wannan dai bangare ne cikin jerin shirye shirye da kungiyar bunkasa diflomisiyya ta kasar Sin CPDA ke gabatarwa, a kuwa wannan karo shirin ya samu halartar 'yan jaridu 29 daga sassan nahiyar Afirka daban daban.

Bisa manufar shirin a cewar mashiryan sa, 'yan jaridun dake halartar sa za su samu zarafi na zagaya sassan kasar Sin, da cibiyoyin watsalabaran kasar daban daban, da masana'antu, su kuma samu zarafin musayar fahimta tsakanin su da masana a fannoni masu yawa.

A wannan gaba da aka fara gudanar da wannan shiri na bana, mun samu zantawa da daya daga 'yan jaridun dake halartar sa daga Najeriya, mai suna Bukola Ogunsina, ma'aikaciya a jaridar Leadership mai helkwata a birnin Abuja gadar mulkin Najeriya.

Da farko dai na fara da tambayar Bukola ko za a yi mana karin haske game da tsare tsaren wannan shiri da suke halartar? Ga kuma abun da take cewa…

Wannan shiri na bana na kushe da 'yan jaridu 29 daga nahiyar Afirka, kuma mun zo nan ne domin kewaya wurare da dama na kasar Sin, ku rubuta rahotanni game da kasar, kusan ina iya cewa shiri ne na ilmantarwa da musaya da kuma kara fahimtar Sin. Yan ciki da abubuwa daban daban a wuri guda. Ina ga shiri ne mai kyau domin yana kunshe da damammakin karfafa alaka tsakanin 'yan jaridu na Afirka da takwarorin su na Najeriya.

Da yake kin zo nan kasar Sin a gababar da aka bude taruka biyu mafiya muhimmanci a kasar Sin, wato taruwan majalissar wakilan al'ummar kasar Sin NPC da na majalissar bada shawara kan harkokin siyasar kasar CPPCC, ko mene ne ra'ayin ki game da tarukan biyu?

Ko da yake bani da kwarewa can game da harkokin da suka shafi siyasa, amma a gani na wadannan taruka sun saba da na sauran kasashe, kamar batun yadda ake mana bita game da tarukan tun daga matakin sanin jam'iyyar dake mulkin kasar, da yadda ake gudanar da tsarin siyasar kasar mai kunshe da wasannan majalissu na wakilan al'ummar kasar Sin NPC, da na majalissar bada shawara kan harkokin siyasar kasar CPPCC. Amma duk da sarkakiyar tsarin a bayyana ta ke cewa tsari ne mai ma'ana. Komai a tsare kuma tarukan na kunshe da cikakkun manufofin da ake so a cimma.

Bukola ta kara da bayyana mana wasu daga abububan da suka kayatar da ita, yayin da take halartar wannan taruka.

Batun kula da muhalli, wato yadda Sin ke maida hankali matuka ga batun kauda matsalar hayaki mai gurbata iska, musamman ganin yadda a baya bayan nan ya zamo cikin muhimman batutuwa da ke jawo hankalin kasashen duniya baki daya. Mutane na ta bayani kan wannan matsala cewa akwai hanyaki mai gurbata iska da yawa a birnin Beijing, kuma akan yi tambaya game da matakin da gwamnati ke dauka game da magance wannan matsala, hakan ya sa ko a yayin wannan taro ma an tabo wannan batu. An bayyana cewa kare muhalli da iska daga gurbata na sahun gaba cikin abubuwan da za a baiwa muhimmanci. Ina ga hakan na da muhimmanci, duba da cewa zai taimaka mutane su nan abun da ake yi don shawa kan matsalar.

Wannan 'yar jarida daga tarayyar Najeriya ta kuma ce duk da ba wannan ne karon farko na zuwan ta kasar Sin ba, wannan zuwa ya sanya tana kallon kasar Sin ta wata mahanga daban, to me mene ne dalili?

Bari na fara da birnin Beijing, a gaskiya dama na taba zuwa nan, amma wannan karon na ga abubuwa da dama da a baya ban lura da su ba, ina iya cewa birni ne da ya hada salon gine gine na sassan turai da Amurka. Birni ne wanda ya ci gaba matuka ta fuskar harkokin sufuri, da gine gine na kawa. Daya daga abokan aikin mu na cewa komai a birnin Beijing na da girma da kayatarwa. Don haka ina ga wuri ne da ya ke da ban sha'awar zuwa.

Da take amsa tambaya game da yanayin aikin idan an kwatanta da gida kuwa, Bukola ta ce aiki ne iri daya

Kusan ba banbanci, tun zuwan mu muna fita ne mu yi kokarin gano batutuwan da ake magana a kan su, mu tantance gaskiya, sannan mu rubuta bayanai ko labarai. Na yi rubuce rubuce da dama musamman game da wadannan taruka na siyasar kasar Sin. Wannan mako ne mai cike da ayyuka don haka mun tura labaru masu yawa. Cikin su na rubuta bayanai kan shirin kasar Sin na kara kudaden inganta tsaro a kasafin kudin kasar Sin wanda ake shirin kara kaso 7 cikin dari. Na kuma yi rubutu kan wannan shiri da muka halarta na CAPC, da yadda aka kara adadin mahalartan sa idan an kwatanta da na bara. Sai kuma batun cigaban tattalin arzikin kasar Sin dake tafiya bisa matsakaicin matsayi, da yadda kasar ta cimma nasarar dorewa kan wannan ci gaba, har a lokacin da ake fama da kalubalen koma bayan tattalin arzikin duniya. Sin ta dore kan matsayin ta kuma har ma tattalin azikin kasar na dada bunkasa a yanzu. Wani malamin jami'a ya bayyana mana cewa, Sin ta samu daidaito a fannin tattalin arziki ne saboda dorewar da ta yi kan manufofin ta na ci gaban kana daukacin 'yan kasar na da manufa daya ne ta ciyar da kasar gaba. Dorewa da kara kwarewa tare da nufin daukacin 'yan kasar na samun ci gaba tare shi ne sirrin.

Bukola ta ce wannan na iya zama darasi ga Najeriya.

Wannan darasi ne gaskiya ga sashen mu na Afirka, musamman ma Najeriya wadda ke ta fadi tashin ta kare bambun ta na kasancewa ta daya wajen karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka. A hannu guda ina ga Najeriya na daukar matakan da suka wajaba domin cimma wannan buri, duba da cewa duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, gwamnatin kasar mai ci na yunkurin ganin hakan ta tabbata. Kamar yadda Sin ke dada bude kofar ta ga kasashen ketare, Najeriya ma na duba abun da take da shi a cikin gida domin fadada ci gaban ta. Don haka dai a wannan bangare Sin na iya zama kyakkyawan misali ga Najeriya. Ka san kamar yadda na ambata a baya batun kula da muhalli yana da muhimmanci. Kuma na yi rubutu kan gudummawar da Sin ke baiwa tattalin arzikin duniya, inda alkaluma suka nuna cewa kasar na baiwa tattalin arzikin duniya kaso 30 bisa dari na ci gaban sa. Lallai hakan babban lamari ne.

A wani bangaren kuma Sin na da burin jawo jarin waje daga sauran kasashen duniya, tana kuma da nufin hadin gwiwa da sauran sassa a bangaren bada hidima, da noma da hakar ma'adanai. Hakan zai yiwa nahiyar Afirka kyau ta yadda sassan biyu za su ci gajiyar juna a wadannan fannoni da na ambata.

Game da sanayyar wannan 'yar jarida da kasar Sin, kin zuwan ta na wannan karo kuwa, ga abun da take cewa.

E, na taba duba labarai game da kasar Sin, an nuna cewa, kasar Sin tana dukufa wajen bude kofa ga waje, kuma tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ina tsammanin cewa, tun da dadewa, kamfanonin kasar Sin sun dade suna zuba jari a kasar Nijeriya, inda suka gudanar da ayyuka iri daban daban. Shi ya sa, zuwana a kasar Sin a yanzu, ba shi ne na farko ba wajen cudanya da mutanen Sin, saboda da akwai Sinawa da dama da suke Nijeriya, wadanda suke ayyuka, da kuma ba da gudummawa a kasar.

To kuma a wannan karo yaya ziyarar ke kasancewa a kasar Sin?

Abun ban sha'awa mutuka shi ne, a karon zuwa na ziyara a kasar Sin bisa gayyatar da kungiyar 'yan jaridu ta kasar Sin ta yi min, mun je wani taron, inda mai jagoran taron ya yi bayani mai ban sha'awa, kuma mai ma'ana sosai. Ya ce mun gaji sosai sabo kokarin mu na gaya wa mutanen duniya "yaya kasar Sin take", shi ya sa, muka gayyace ku zuwa nan kasar Sin, domin ku duba da kanku, babu bukatar mu yi muku bayani kan kasar Sin.

Ko akwai abun da ya fi burge ki a yayin wannan ziyara?

"Tsari, komai a tsare yake, a zahiri ana gudanar da ayyuka iri daban daban a nan kasar Sin yadda ya kamata. Kasar Sin kasa ce mafi yawan mutane a nan duniya, ta dukufa sosai wajen daidaita harkoki daban daban a kasar, abin da ya burge ni kware da gaske.

Malama Bukola ta kuma yi mana bayani game da yadda ta samu wannan dama ta sake ziyartar kasar Sin?

Ofishin jakadanci na kasar Sin ya gayyace ni, sabo da wasu labarai da sharhin da na taba rubutawa a jaridar Leadship, dangane da ziyara ta a kasar Sin a karo na farko, na rubuta dukkan abubuwan da na ji da kuma wadanda na gani a kasar Sin, akwai harkokin kasuwanci da kuma al'adu da dai sauransu, musamman ma a fannin al'adu, sabo da galibin mutanen Nijeriya ba su san kasar Sin sosai ba, waso ma ba su taba gani "Jajayen fitulu ba", da kuma ma'anarsu. A karon farko da na kawo ziyara a nan, wadannan Jajayen fitulu sun ba ni sha'awa sosai, kuma, abokan na Sinawa su gaya mini cewa, Jajayen fitulu suna wakiltar wata alama ce ta jin dadi, da kuma fatan samun sa'a a nan kasar Sin, lamarin da ya sa, bayan komawa ta Najeriya, na rubuta abubuwa da dama game da kasar Sin, sabo da sun ba ni sha'awa sosai.

To ko wadanne irin batutuwa kika fi son rubuta bayani a kan su game da kasar Sin?

Dukkansu, dukkan harkoki game da kasar Sin, sabo kasar Sin wani littafi ne mai girma, kaman al'adu, siyasa, kasuwanci da dai sauransu. Wani shehun malami ya taba bayyana mana cewa, idan ka ziyarci kasar Sin na makwani da dama, za ka sami abubuwa da dama da za ka iya rubutawa, idan ka ziyarci kasar Sin na watanni da dama, za ka iya rubuta wani littafi, amma idan ka zauna a kasar Sin tsawon shekara guda daya, ba za ka iya rubuta komai ba, sabo da lallai akwai abubuwa da yawa da ka karu da su, ta yadda za ka ma rasa wanda za ka bayyana.

Na taba zuwa nan kasar Sin na yi kwanaki goma, na ziyarci wurare da dama, kamar su Beijing, da Chongqing da kuma Guangdong, na kuma rubuta abubuwa da yawa kan ziyara ta a wuraren.

Mun kuma tambaye ta abubuwan da take fatan yi a ziyarar ta wannan karo

A wannan karo, bisa tsarin zaman mu zan ziyarci wasu wurare na tarihi a birnin Beijing, sa'an nan, zan kai ziyara birane daban daban na kasar Sin, kuma zan ci gaba da rubuta wasu labarai, da rahotanni game da kasar Sin, wannan shi ne ma'anar ziyara ta a wannan karo nan kasar Sin. Za mu kara saninmu game da zamatakewar al'ummomin kasar Sin, ba kawai ziyara da za mu yi a nan kasar ba, har ma za mu karu sosai, sabo da za mu koyin yaren Sinanci, mu ziyarci wurare daban daban, za mu kuma rubuta abubuwan da muka gani a lokacin ziyarar mu a nan kasar cikin watanni goma masu zuwa.

Hakika dai, cikin makwanni biyu da suka gabata, na riga na rubuta rahotanni kimanin guda shida, game da taruka biyu da ake yi a nan kasar Sin a halin yanzu, don mun halarci wasu taron manema labarai, a nan gaba kuma, za mu halarci taron BRICS da za a yi a kasar, da wasu taruka na daban daba. Ko shakka babu za su taimaka matuka wajen kara saninmu game da kasar Sin, bisa fannoni daban daban, kamar tattalin arizki da zaman takewar al'umma da dai sauransu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China