170322-Muhimman-tarukan-kasar-Sin-na-shekarar-2017.m4a
|
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, majalisa ce da ta kunshi mambobi daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da jam'iyyun siyasa, kungiyoyi da wakilai daga bangaren kwararru har ma da sassa masu zaman kansu.
Bisa al'ada, jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar ce ke da wakilai mafi rinjaye a majalisar, inda take da kashi 1 bisa 3 na daukacin mambobin majalisar. Sauran mambobin majalisar sun fito ne daga jam'iyyun da ke kawance da jam'iyyar kwaminis mai mulki da sauran wakilai masu zaman kansu wadanda ba sa cikin kowace jami'yya.
A daya hannun kuma majalisar wakilan jama'a wato NPC a takaice majalisa ce da ake zaben wakilanta daga mazabun gundumomi, yankuna masu 'yancin gashin kansu, birane karkashin kulawar gwamnatin tsakiya, rundunar sojojin kasar.
Aikin majalisar wakilan sun hada da gyaran kundin tsarin mulkin kasa da sanya ido wajen ganin an aiwatar da tanade-tanaden da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Bugu da kari, aikin majalisar ce ta bullo da dokoki da suka shafi manyan laifuffuka, harkokin jama'a, hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran batutuwan da ke shafar rayuwar Sinawa.
Har ila yau, majalisar wakilan ce take zabe da kuma nada wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati da yanke hukunci game da manyan batutuwan da suka shafi kasa baki daya. A tarukan na bana, mahukuntan kasar Sin sun kudurin cimma kaso 6.5 cikin 100 na GDPn kasar a wannan shekara, da samar da guraben ayyukan yi miliyan 11 da taimakawa tsofaffi dake zaune da yaransu, da rage talauci, da kare muhalli, da kara inganta tsaro da sauran matakai na inganta rayuwar al'ummar Sinawa.
Sauran sun hada da manufofin diflomasiyar kasar Sin, shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da kara samarwa wakilci adadin kujeru a majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da sauransu. (Saminu, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)