170315-Shawarwarin-da-aka-gabatar-a-taron-CPPCC-na-kasar-Sin-na-bana.m4a
|
Rahotanni sun bayyana cewa kashi 34.72 cikin dari na shawarwarin, sun shafi raya tattalin arziki ne, yayin da kaso 11.67 cikin dari suka shafi raya harkokin siyasa, sai kuma kaso 7.99 cikin dari da ke shafar al'adu. Kaza lika kaso 35.49 cikin dari shawarwari ne da suka jibanci raya al'umma, yayin da kaso 10.13 cikin dari na wadannan shawarwari sun shafi kiyaye muhalli.
Masu fashin baki na cewa,duk kan shawarwarin da wakilan suka gabatar suna da tasiri matuka ga rayuwar al'ummar Sinawa da ma duniya baki daya. Kuma wannan ya kara tabbatar da kudurin kasar Sin na ba da gudummawa ga harkokin kasa da kasa daga dukkan fannoni. (Ahmed, Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)