in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata a bana
2017-03-15 10:20:09 cri

A jiya Talata ne, hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluman ci gaban tattalin arzikin kasar na watanni 2 na farkon shekarar bana wato shekarar 2017, inda aka bayyana cewa, a cikin wadannan watanni, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata.

Kakakin watsa labarai na hukumar kididdigar kasar Sin, kana babban masanin tattalin arziki Sheng Yunlai ya bayyana cewa, a watan Janairu da kuma watan Fabrairun bana, ma'aunan tattalin arzikin kasar Sin suna da kyau, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, ko na watanni biyu na karshen shekarar bara wato watan Nuwamba da na Disamban bara, wasu ma'aunan sun kyautata fiye da hasashen da aka yi. Sheng Yunlai ya kara da cewa, a takaice dai, ana iya ganin ci gaban tattalin arzikin da aka samu daga yadda alkaluman suka sauya a fannoni uku, yana mai cewa, "Sauyi na farko shi ne, tattalin arzikin kasar Sin yana gudana lami lafiya, misali, kamfanonin kasar suna cike da kuzari, kuma suna samun babbar riba, kana ana kara zurfafa kwaskwarima a tsarin tattalin arzikin, musamman ma a fannin samar da kayayyaki, a saboda haka, muhallin kasuwanni yana kara kyautatuwa a kai a kai, kuma huldar dake tsakanin masu samar da kayayyaki da masu kera kayayyaki ita ma ta kyautata. Sauyi na biyu kuwa, an samu babban ci gaba wajen yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, na uku, an samu sakamako a bayyane, musamman ma yayin da ake tafiyar da harkokin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare."

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, adadin jarin da aka zuba kan kadarorin kasa a watanni 2 na farkon bana ya karu, kana adadin jarin da 'yan kasuwa suka zuba ya karu cikin sauri, inda ya kai kaso 6.7 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, haka kuma ya karu da kaso 3.5 bisa dari idan aka kwatanta shi da na tsawon shekarar bara, a hakika, tun daga watan Maris na bara har zuwa yanzu adadin ya kasance a sahun gaba.

Wannan rana ita ma hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da wani sabon ma'aunin tattalin arziki, wato alkaluman aikin samar da hidima, wanda zai nuna mana sauyin da aka samu a cikin gajeren lokaci. Sheng Yunlai ya bayyana cewa, "Wannan shi ne karo na farko da muka fitar da wannan alkaluma game da aikin samar da hidima, to, mene ne dalilin da ya sa muka yi haka? Makasudinmu shi ne domin muna son nunawa al'ummar kasar sauyin da aka samu a fannin aikin samar da hidima a cikin gajeren lokaci daga dukkan fannoni, wannan zai taimaka mana wajen tsara manufofin da za su dace domin biyan bukatun kamfanonin samar da hidima, tare kuma da nuna wa al'ummar kasa yanayin da aikin ke ciki a halin yanzu, da kuma ci gaban da ake samu a wannan fannin a kasar Sin. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, aikin samar da hidima ya kara taka muhimmiyar rawa, wanda ya zarta kaso 50 bisa dari cikin tattalin arzikin kasar Sin. Sai dai kuma an fuskanci wasu matsaloli yayin da ake gudanar da bincike da kididdiga kan wannan aikin, saboda aikin ya kunshi sana'o'i da yawa, kana yanayin da aikin ke ciki ya kan sauya cikin sauri, shi ya sa wajibi ne mu kara kokari a wannan aikin."

Game da sabbin alkaluman tattalin arzikin da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar, babban mai ba da shawara kan zuba jari na kamfanin hada-hadar kudi na Xiangcai Hong Shumin ya bayyana cewa, hakan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba, yana mai cewa, "Daga alkaluman da aka samu a watanni 2 na farkon bana, ana iya cewa, watakila kasar Sin za ta cimma burinta na samun karuwar GDP da kaso 6.5 bisa dari a bana cikin sauki, wato kafin watan Yunin bana, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun karuwa yadda ya kamata, dalilin da ya sa haka shi ne domin an gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin kasar, musamman ma wajen samar da kayayyaki."

Ban da haka, kakakin watsa labarai na hukumar kididdigar kasar Sin, kana babban masanin tattalin arziki Sheng Yunlai shi ma ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasashen duniya yana fuskantar tangarda, kasar Sin ita ma tana fuskantar kalubale yayin da take yiwa tsarin tattalin arzikinta kwaskwarima, a saboda haka nan gaba, kamata ya yi mu nace ga sabon tunanin samun ci gaba, tare kuma da kara zurfafa kirkire-kirkire, ta yadda za a ciyar da tattalin arzikin kasar ta Sin gaba ba tare da wata matsala ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China