in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama wajibi a fadada kandagarkin yaduwar cutar HIV zuwa yankunan kudu da hamadar sahara
2017-03-14 20:38:42 cri
Tsohon minsitan lafiya a Namibia Richard Kamwi, ya ce ya zama wajibi a fadada ayyukan kandagarkin yaduwar cutar HIV, zuwa yankunan kudu da hamadar sahara

Mr. Kamwi wanda ya fadi hakan ta cikin wata sanarwa da aka fitar a yau din nan. Ya ce daukar wannan mataki ya zama dole, muddin dai ana fatan shawo kan yaduwar wannan cutar mai hadari a dukkanin sassan duniya baki daya.

Kamwi dai ya jaddada ra'ayin da dama daga mahalarta wani taro, na zakulo hanyoyin yaki da cutar HIV da ya gudana a Namibia tsakanin ranekun 8 zuwa 10 ga watan nan na Maris.

Yayin taron da ya gabata dai mahalartan sa, sun bayyana muhimmancin daukar matakan kandagarki ga al'ummun dake cikin hadarin kamuwa da wannan cuta, suna masu cewa akwai bukatar zage damtse wajen kau da shinge, da ke dakile yunkurin da ake yi na dakatar da yaduwar cutar. Yayin da a hannu guda ake ci gaba da yiwa wadanda suka kamu da cutar magani.

Yanzu haka dai yankin kudancin saharar Afirka na kan gaba da kaso 70 bisa dari, na masu dauke da cutar HIV, wanda hakan ya sanya yanki zama na daya a wannan fanni, tsakanin sauran sassan duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China