in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawancin mutane suna goyon bayan aikin mata
2017-03-08 10:40:03 cri

Yau Laraba 8 ga wata ce ranar mata ta duniya, a kuma wannan rana, hukumar 'yan kwadago ta kasashen duniya wadda hedkwatarta a birnin Geneva ta fitar da wani rahoton bincike, inda a karo na farko, ta gabatar da cikakkun alkaluma, game da ra'ayoyin da ake samu kan aikin mata tsakanin jinsunan biyu. Rahoton dai na nuna cewa, da dama daga maza suna goyon bayan aikin mata.

Hukumar 'yan kwadago ta kasashen duniya, da shahararren kamfanin bincike na Gallup sun gudanar da wannan bincike ne cikin hadin gwiwa, taken rahoton da aka fitar bayan binciken shi ne "Samar da makoma mai haske ga matan da suke aiki: muriya daga mata da maza."

An gudanar da wannan bincike ne ga mutane kusan dubu 150 dake kasashe da yankuna 142. Alkaluman da aka samar bayan binciken da aka gudanar sun nuna cewa, mata kaso 70 bisa dari, da maza kaso 66 bisa dari, suna goyon bayan mata su fita waje samun aikin yi domin karbar albashi.

A bangaren mata kuwa kan batun, mata kaso 29 bisa dari sun fi son fita waje aiki domin samun kudi, kana kaso 41 bisa dari sun fi son yin aiki a waje tare kuma da kula da iyalinsu, yayin da kaso 27 bisa dari kacal suka bayyana cewa, suna son hutu a gida ko kula da iyali kawai. Wato ba su so su fita waje su yi aiki.

Abu mai muhimmanci dai shi ne, an samu wannan sakamakon bincike ne daga mutane da dama a fadin duniya, ciki har da matan dake kasashen Larabawa. Kana wani abun mai faranta ran mutane shi ne, babu banbanci tsakanin ra'ayin da maza suke da shi kan batun da na matan, duba da cewa, rahoton ya nuna cewa, maza kaso 29 bisa dari suna goyon bayan mata su yi aiki a waje, kaso 38 bisa dari kuma suna fatan mata za su iya yin aiki a waje tare kuma da kula da iyalinsu, yayin da kaso 29 bisa dari kacal ne ke fatan mata za su kula da iyali kawai.

Ban da haka kuma, rahoton binciken ya nuna cewa, maza da mata wadanda suka kammala karatu a jami'a, sun fi son mata su yi aiki a waje, tare kuma da kula da iyali.

Amma game da wannan batu, wato mata su yi aiki a waje, an fi mai da hankali kan matsalar da ake fuskantar, wato idan mata suna aiki a waje, to, wace ce za ta kula da iyali? Ko yaya matan dake aiki a waje suke iya kula da yara da iyali baki daya? A hakika dai, yawancin maza da matan da suka shiga binciken sun gabatar da wannan tambaya. Kana mai yiwuwa mata su gamu da matsaloli a wuraren aiki, alal misali, rashin adalcin da ake iya nuna musu wajen samun damammakin aiki, da kudin shiga, da damun da maza suke musu a wurin aiki da dai sauransu.

Kaza lika, akwai banbanci tsakanin ra'ayoyin da mata suke dauka, bisa dalilin shekarun haihuwarsu. Ga misali, matan dake da shekarun haihuwa tsakanin 15 zuwa 29 sun fi gabatar da tambayoyi game da rashin adalci wajen samun damammakin aiki, da zalunci, da damun da suke gamuwa da shi a wurin aiki. Kana matan dake da shekarun haihuwa tsakanin 30 zuwa 44 sun fi ba da muhimmanci kan batu game da yadda za su kula da yara da kuma iyali. Saura kuma, wato matan da shekarun haihuwarsu suka zarta 45 sun fi mai da hankali kan kudin shiga.

Ana iya cewa, kusan babu banbanci tsakanin ra'ayoyin da ake dauka kan hakan a fadin duniya. Wato dai maza da mata dukkansu suna ganin cewa, idan mace da wani namiji suna da matsayin ilimi da fasahar aiki iri daya, to kamata ya yi su samu damar aiki iri daya. Kana mata kaso 25 bisa dari, da maza kaso 29 bisa dari suna ganin cewa, mata sun fi samun sauki yayin da suke neman aiki, amma alkaluman da aka samar sun bayyana cewa, kawo yanzu, akwai banbancin jinsi a kasuwannin 'yan kwadagon kasashen duniya.

Babban jami'in hukumar 'yan kwadagon kasashen duniya Guy Ryder ya bayyana cewa, sakamakon binciken ya nuna cewa, yawancin maza da mata a fadin duniya suna sa kaimi ga mata da su yi aiki a waje, kuma hakan zai taimakawa ci gaban aikin mata. A sa'i daya kuma, zai sa kaimi ga maza da su yi aikin gida. Wanda hakan shi ma zai taimaka wajen tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata yayin da suke aiki.

Shugaban kamfanin Gallup, kana jagoran kamfanin Jim Clifton, shi ma ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata a fadin duniya, a saboda haka ya fi dacewa a samar da damammakin aiki ga mata, lamarin dake shafar moriyar mata, gami da moriyar bil Adama baki daya. (Jamila)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China