170305-Kasar-Sin-ta-samu-saurin-bunkasuwa-a-fannin-horar-da-matasa-fasahohin-kwallon-kafa-a-makarantu-Bilkisu.m4a
|
A watan Febrairun da ya gabata, an shirya wani taron manema labaru a nan birnin Beijing, wanda ma'aikatar kula da harkokin ilmi ta shirya tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, ciki har da hukumar kwallon kafa ta Sin wato CFA a takaice, inda aka gabatar da yadda ake shirya kwas-kwasan horas da harkar kwallon kafa a makarantu da shirya gasa tsakanin daliban makarantu a tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ya zuwa yanzu, an kafa makarantun horas da kwallon kafa sama da dubu 13 a nan kasar Sin, kuma bisa shirin da aka yi, an ce ya zuwa shekrar 2025, za a horar da matasa fasahohin kwallon kafa sama da miliyan 50 a makarantun. Shin, irin karin kwararru da ake samu a fannin kwallon kafa za su iya kawo bunkasuwar harkar kwallon kafan kasar Sin ko a'a? Kuma yaya za a daidaita matsayi a fannin aikin kwallon kafa na makarantu da na kungiyoyin wasan kwallon kafa? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani kan wannan batu.