in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RA'AYINA AKAN WANNAN TARO NA NPC DA AKA BUDE DA KUMA MAGANAR TATTALIN ARZIKI
2017-03-06 09:41:58 cri
Abin da kowace kasa take takama da shi shine arziki da tattalinshi, karfi na soji, ilimin kimiyya da sana' oi, noma da masana'antu. amma abin da yake gaba awannan karnin namu shine, idan kasa na da arzikin tattalin arzikin kasa, to zata iya samun duka sauran. wannan taro na shekara-shekara na majalisar wakilan mutanen Sin da kuma masu bada shawarwari akan siyasa, taro ne wanda zai kara karfafa tattalin arzikin da kuma harkar siyasa ta kasar ta Sin. shekara wacca ta wuce ta 2016, gudun ruwan arzikin na kasar da aka samu na GDP shine 6.7% na ci gaba.

A wannan taro kuma na wannan shekarar, shuwagabannin jama ar Sin sun ce zasu rage gudun ruwan tattalin arzikin sabo da wayannan dalilan: na daya akara samar da dorewa a cikin tattalin arzikin, na biyu a kara samar da ayyukan yi, na uku shine a rage kasada da ka iya faruwa a cikin bangaren arzikin kasar na wannan shekara, na hudu shine a kara wa kudun kasar daraja na dorewa kar kudin su zama sun kamu da hadari a cikin sauran kudade na duniya. menene abin la'akari anan? abin da yakamata duk wani mai hankali da lura, imma dai yana cikin gwamnatine ko kuma yana cikin wanin haka, ya kamata tunaninsa ya koma ga samar wa da kasa hanyoyi na ci gaba. ita kuma wannan kasa ta Sin, ta daukanwa mutanenta alkawarin karesu, samar da ci gabansu ta hanyoyi daban daban. wannan shine yasa kasar take ta aiki matuka gaya wajen cika wannan alkawura tsakaninta da jama'arta.

Wani kuma da ya kamata mu gane shine, duk abin da kaga kasar sin tayi musamman ma wajen maganar tattalin arziki, to fa akwai walaki saboda tabbas hakan zai kawo alfanu ne ga kasar. sabo da hakane ma kasashe da dama na duniya suke so suna kallo da nazari akan yarda kasar ta Sin ke gudanar da al'amuranta, sannan sume su kwaikwaya daga gare. zamu ci gaba da baku albarkacin bakin mu a yarda muke fahimtar al'amura da ke tafiya a wannan taro da wasu ma bayan wannan. Naku,

Dr. Sheriff Ghali Ibrahim,

Jami'ar Abuja,

tarayyar Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China