in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An maida hankali ga fannoni biyar a cikin manufofin hadin gwiwar kasa da kasa da suka shafi yanar gizo
2017-03-02 21:02:26 cri
Da safiyar yau Alhamis 2 ga watan nan ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta gudanar da taron manema labaru na gida da waje a nan birnin Beijing, inda aka yi bayani game da manufofin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin yanar gizo da aka gabatar a jiya.

Jami'in lura da harkokin yanar gizo na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Long Zhou, ya maida hankali ga fannoni biyar, yayin da yake bayani game da batun.

Na farko, ya ce Sin na fatan samun bunkasuwa cikin lumana. Wato kasar na fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da kasa da kasa, wajen tabbatar da tsaron yanar gizo, bisa tushen girmama juna. Na biyu kuma za ta hada kai da samun moriya tare da sauran kasashen. Ya ce Sin na son yin kokari tare da kasa da kasa, wajen cimma burin kiyaye tsaro da samun wadata tare a harkokin da suka jibanci yanar gizo, bisa tunanin hada kai da samun moriyar juna.

Na uku kuma akwai batun samar da daidaito game da ikon mallaka. Ya ce kamata ya yi kasa da kasa su yi hadin gwiwa bisa tushen girmamawa ikon mallakar ko wace kasa. Na hudu kuma a ci moriyar fasahohi. Sin tana son ci gaba da yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasa da kasa a fannonin kiyaye tsaro da more fasahohin yanar gizo. Sai na biyar, wato share fagen kafa tsari da kyautata shi tare. A nan ya kamata a kafa tsarin kula da yanar gizo na duniya mai tsari na demokuradiyya, da adalci, wanda ke shafar sassa daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China