in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karon farko kasar Sin ta halarci bikin nune-nunen kayayyaki masu ratsa sararin samaniya da ake yi a kasar Australiya
2017-03-01 11:31:46 cri

A jiya, 28 ga watan Faburairu ne, aka kaddamar da bikin nune-nunen kayayyaki masu ratsa sararin samaniya a wani filin jirgin sama na Avalon dake birnin Melbourne na kasar Australiya. Wannan shi ne karon farko da kasar Sin ta halarci wannan biki, inda ta baje kolin rokokinta iri iri, domin neman izinin shiga kasuwannin sararin samaniya na duniya, da kuma neman sabon salon yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya.

Dandalin nune-nunen kayayyaki masu ratsa sararin samaniya na kasar Sin yana wani kyakkyawan wurin dake cikin dakin baje kolin. Mr. Meng Xiang, wani ma'aikacin kamfanin nazari da samar da kayayyaki masu ratsa sararin samaniya na kasar Sin ya bayyana yadda kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasar Australiya a fannin yin amfani da irin wadannan kayayyaki. Meng Xiang yana mai cewa,"Ko da yake wannan ne karon farko da muka halarci wannan biki. Amma a tun shekarun 1990 muka soma yin hadin gwiwa da kasar Australiya. A wancan lokaci, rokokin dankon kaya kirar kasar Sin sun soma shiga kasuwannin kasashen duniya, kuma kasar Australiya ita ce a kan gaba wajen sayen kayayyakinmu."

Dalilin da ya sa kasar Sin ta yi nune-nunen sabbin kayayyaki masu ratsa sararin samaniya a wannan biki, shi ne bayyana wa kasashen duniya karfin nazari da kuma samun sabbin fasahohin rokokinta, da karfinta na harba da kuma tabbatar da ingancin kayayyaki masu ratsa sararin samaniya dake a kan hanyarsu a sararin sama. Bugu da kari, tana son neman sabuwar hanyar yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, ta yadda za ta iya samun wani sabon salon shigar da kayayyakinta a kasuwannin kasa da kasa dake iya biyan bukatun masu yin amfani da kayayyakinta.

Mr. Li Tongyu, shugaban wani sashen kamfanin nazari da kuma samar da kayayyaki masu ratsa sararin samaniya na kasar Sin yana mai cewa, "A shekarar 2015 da 2016, mun samu nasarar harba rokokin dankon kaya na Long March mai lamba 5 da Long March mai lamba 7 da kuma Long March mai lamba 11. Kawo yanzu, mun kai wani sabon matsayi a fannin nazarin fasahohin zamani kan rokokin dankon kaya, karfinsu na dankon kaya ma ya ninka sau da dama."

A 'yan shekarun baya, kasuwannin kayayyaki masu ratsa sararin samaniya sun samu ci gaba sosai. Sakamakon wasu manufofin kasar Amurka, yanzu kasar Sin ba za ta iya harba taurarin dan Adam dake da kananan na'urorin gyara kirar Amurka ba. Amma yanzu bisa shirin bunkasa "ziri daya da hanya daya" da tsarin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da sauran kasashen duniya, kasar Sin na kokarin yin amfani da rokokin dankon kaya wajen bunkasa fannin yin amfani da kayayyaki masu ratsa sararin samaniya, wato taimakawa kasashe wadanda suke bukatar kayayyaki masu ratsa sararin samaniya wajen kera da harba irin wadannan kayayyaki zuwa sararin sama da kuma yin amfani da su a wadannan kasashe. Sabo da haka, kamfanonin kasar Sin suna ba da hidimar harba da kuma fitar da taurarin dan Adam da suka kera, ko samar da fasahohin kayayyaki masu ratsa sararin samaniya ga kasashen da suke bukata, har ma suna taimaka musu wajen horas da ma'aikata da gina dakunan sarrafa irin wadannan kayayyaki masu ratsa sararin samaniya. Mr. Li Tongyu ya kara da cewa, "A cikin shekaru biyu da suka gabata, bi da bi mun taimakawa kasashen Laos da Belarus wajen harba taurarin dan Adam. Musamman, mun samar wa kasar Laos tauraron dan Adam da muka kera, da kuma koyar musu fasahohin yin amfani da shi, kana mun zuba jari tare da kafa wani kamfani tare da kasar ta Laos domin yin amfani da wannan tauraron dan Adam yadda ya kamata."

Bugu da kari, a watanni 6 na farkon wannan shekara, a lokacin da take tafiyar da aikin sufurin 'yan sama jannati zuwa sararin sama, kasar Sin za ta harba rokar dankon kaya ta Long March mai lamba 7 domin sufurin kayayyakin yau da kullum zuwa sararin samaniya. Karfin rokar dankon kayan zai iya biyan bukatun da ake da su a kasuwa. Sannan a karshen watanni 6 na shekarar bana, za a yi amfani da rokar Long March mai lamba 5 wajen harba kumbon Chang'e mai lamba 5 zuwa duniyar wata. Game da kayayyaki masu ratsa samaniya da kamfanin kasar Sin ya nuna a bikin, Mr. Darien Colbeck, wani manazarcin bikin na kasar Australiya ya nuna cewa, "Kasashen Amurka da Rasha sun taba yin fice a fannin kasuwar kayayyaki masu ratsa sararin samaniya Yanzu kasar Sin ta yi fitar barden guza, inda ta samu wasu sakamakon dake jawo hankulan al'ummar duniya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China