170227-Ci-gaban-duniya-na-bukatar-kimiyya-kimiyya-na-bukatar-hanayen-mata-Kande.m4a
|
Bambancin jinsi a fannin kimiyya da fasaha ya riga ya zama wani babban cikas ga ci gaban duniya. Wani abin farin ciki shi ne, an riga an gano matsalar da muhimmancin warwarewarta. Don Haka bisa hadin gwiwar hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO da hukumar Majalisar mai kula da al'amuran mata da kuma wasu hukumomi dake goyon bayan shigar da mata a dukkan matakai cikin harkokin kimiyya da fasaha da ilimin injiniya da lissafi, a ranar 15 ga watan Disamban 2015, MDD ta amince da ware ranar 11 ga watan Fabrairun ko wace shekara a matsayin ranar tunawa da mata dake nazari ko aiki a fannonin kimiyya da fasaha ta duniya, domin jinjinawa irin rawar da suke takawa ga ci gaban bangaren. Har ila yau, ranar na da nufin yaki da duk wani nau'in bambancin jinsi da ake nunawa mata wajen neman ilimi, aiki, shari'a ko zaman takewa, tare da ciyar da ilimi, manufofi da shirye-shiryen kimiyya gaba, ta yadda mata za su shiga a dama da su har ma su kai ga cimma nasarori.(Kande Gao)