in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran ganawar shugabannin da za a gudanar a Xiamen za ta zurfafa huldar abokantaka tsakanin kasashen BRICS

2017-02-24 12:41:58 cri

A jiya Alhamis 23 ga watan nan ne, aka gudanar da taro karo na farko na masu aikin shiga tsakani na kasashen mambobin kungiyar BRICS na shekarar 2017, taron da ya gudana a birnin Nanjing dake lardin Jiangsu na kasar Sin. Wannan dai ya nuna cewa, an riga an fara shirya ganawar shugabannin kasashen da za a gudanar a birnin Xiamen na lardin Fujian ta kasar ta Sin a watan Satumba mai zuwa.

Ganawar da za a gudanar tsakanin shugabannin kasashen mambobin kungiyar BRICS a birnin Xiamen a watan Satumba mai zuwa, muhimmin aiki ne na diplomasiyya da kasar Sin za ta gudanar a bana. A saboda haka gwamnatin kasar ta Sin ke sa ran samun babban sakamako a yayin wannan ganawa.

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, wanda kuma ya halarci bikin bude taron na masu aikin shiga tsakani na kasashen BRICS, a karo na farko a bana a birnin na Nanjing ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin kungiyar BRICS zai kara karfafuwa, bisa tushen samun moriyar juna ba tare da rufa rufa ba, kana zai taka rawa wajen kafa wani dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen kudanci, tare kuma da kafa wani tsari na kasa da kasa mai cike da adalci.

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017, a hukumance kasar Sin ta shiga jerin kasashen dake rike da shugabanci na karba karba, inda za ta shirya ganawa tsakanin shugabannin kasashen mambobin kunigyar BRICS karo na 9 a birnin Xiamen, a watan Satumba mai zuwa yadda ya kamata. Kana an gudanar da taron masu shiga tsakani kasashen karo na farko a jiya Alhamis a birnin Nanjing. Yayin bikin bude taron, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru goma da suka gabata, tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen BRICS ya riga ya kasance alama a fannin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Yana mai cewa, "A cikin shekaru goma da suka gabata, kasashen BRICS sun yi matukar kokari, wajen inganta hadin gwiwa dake tsakaninsu, ta yadda ya kasance alama ta fannin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ana iya cewa, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin kasa da kasa, da kuma tunkatar kalubale a fadin duniya. Kana hakan ya dace da moriyar daukacin al'ummomin kasashen duniya. Ban da haka kuma, zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya."

Bisa alkaluman da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar, an ce a shekarar 2016, kasashen da suka samu saurin ci gaban tattalin arziki, da kasashe masu tasowa, kamar kasashen mambobin kungiyar BRICS, sun ba da babbar gudummawa kan karuwar tattalin arzikin duniya, wanda ya kai kaso 80 bisa dari. Kana a cikin shekaru goma da suka gabata, kasashen BRICS su ma sun taka muhimmiyar rawa, wajen bunkasar tattalin arzikin duniya, wanda ya zarta kaso 50 bisa dari.

Sai dai a halin da ake ciki yanzu, kasashe daban daban dake fadin duniya, na fuskantar yanayi maras tabbas a fannin siyasa da kuma tattalin arzikin baki daya, don haka ya zama wajibi kasashen BRICS, su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin tunkarar kalubale tare. Yang Jiechi ya bayyana cewa, "Kasashen BRICS suna ba da jagoranci kan aikin gudanar da harkokin duniya, saboda haka kamata ya yi su ci gaba da sauke nauyi dake kansu, na kara ba da gudummawa, wajen tunkarar kalubale. A sa'i daya kuma, su yi kokarin kafa wata duniyar bil adama mai makoma daya, tare da sauran al'ummomin kasashen duniya. Ta haka ne za a iyar cimma burin kyautata aikin gudanar da harkokin duniya ta hanyar shawarwari, da kuma samun moriyar juna."

An kafa tsarin masu aikin shiga tsakani ne domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS cikin lumana. Kuma muhimmin aikinsu shi ne share fage a fannin siyasa, kafin ganawar shugabannin kasashen kungiyar, kuma a ko wace shekara, ana shirya taruka da daman a wannan rukuni. A yayin wannan taro na birnin Nanjing, masu aikin shiga tsakani, da jakadun kasashen dake wakilci a kasar Sin, da wakilan bankin raya kasashen BRICS, za su tattauna kan taken "zurfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS domin samun makoma mai haske".

A yayin taron, za a tattauna kan ci gaban da aka samu wajen hadin gwiwa tsakanin sassan, musamman ma a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu.

Mataimakin shugaban hukumar kula da huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta kasar Afirka ta Kudu Anil Sooklal, kana mukadashin mai aikin shiga tsakani kan harkokin kasashen BRICS ya bayyana cewa, "Taken da kasar Sin ta gabatar game da ganawar shugabannin kasashen BRICS, wato 'zurfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS domin samun makoma mai haske', yana da babbar ma'ana, dalilin da ya sa haka shi ne, kasancewar hadin gwiwa yana da muhimmanci matuka, musamman ma hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa."

Shi ma jami'in aikin na shiga tsakani kan harkokin kasashen BRICS na kasar Rasha, kana mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergey Ryabkov, ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin take kasancewa mai rike shugabancin karba karba, ko shakka babu, hadin gwiwa dake tsakanin kasashen BRICS zai shiga wani sabon matsayi. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China