170301-Ababan-hawa-masu-amfani-da-wutar-lantarki-na-kara-karbuwa-a-Sin.m4a
|
A cewar hukumar ta NEA, a shekarar 2016 da ta gabata an samar da irin wadannan na'urorin caji har 100,000, wanda hakan ya sanya adadin irin wadannan cibiyoyi zuwa150,000.
A shekarar ta bara nau'o'in ababen hawa masu aiki da wutar lantarki a cikin kasar ta Sin, sun zuki lantarki da ya kai na sa'o'i daidai da kilowatt biliyan 1.2, matakin da ya bada damar tsumin man fetur da ake konawa har tan 400,000.
Bisa tanadin shirin shekaru biyar-biyar na kasar Sin, wato tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, an tsara gina cibiyoyin cajin ababen hawa masu aiki da wutar lantarki a sassa daban daban, wadanda za su ishi irin wadannan ababen hawa miliyan 5.
Masu fashin baki na cewa, wannan wani babban ci gaba ne a kokarin da kasar Sin ke yi na bunkasa sana'ar kera motoci da sauran ababen hawa masu aiki da wutar lantarki. Bugu da kari, wannan mataki a cewar masana, wani bangare ne na alkawarin da mahunkuntan kasar Sin suka yi game da yadda za a kara rage gurbatar muhallin duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanisu Chen)