170222-Bunkasuwar-harkokin-kasuwanci-ta-Intanet-a-kasar-Sin.m4a
|
Yanzu haka wannan harka ta kara bunkasa a sassa daban-daban na duniya, ciki har da nan kasar Sin, inda bayanai ke nuna cewa, jama'a sun fi son yin sayayya ta intanet maimakon zuwa shaguna ko kanti.
Sai dai kuma yayin da wasu ke maraba da wannan tsari wasu kuma na nuna dari-darin amfani da shi, saboda abin da suka kira tsoron 'yan damfara. Wannan ya sa hukumomi a lokuta da dama ke kira da a kara daukar matakai daban-daban don tabbatar da tsaron intanet.
Manyan kamfanoni da suka shahara a duniya a wannan harka sun hada da AliBaba da JD da T-mall da Taobao da Amazon da sauransu.
Harkar sayayya ta yanar gizo ta haifar da wanzuwar kamfanonin jigilar kayayyaki irinsu SF, da STO, da ZTO, da YTO, da BEST da makamantansu, wadanda kamfanonin hidima ko jigilar kayayyaki sun samar da tarin guraben ayyukan yi ga jama'a galibinsu matasa.
Masu fashin baki na cewa, tsarin sayar da kayayyaki ta intanet yana saukaka bukatan jama'a ta fannin sayayya, duba da yadda jama'a ke da zabi na kanti ko kayan da suke son saya saboda saukin farashinsa da rashin bata lokaci. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)