in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana da hangen nesa wajen kiyaye moriyar dan Adam, in ji shugaban taron kwamitin raya zamantakewar al'ummar MDD karo na 55
2017-02-21 12:09:08 cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, shugaban taron kwamitin raya zamantakewar al'umma na MDD karo na 55 Philip Chaves, ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, inda ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, al'ummomin kasashen fadin duniya suna kara dogaro da juna, kuma suna fuskantar kalubale mai tsanani iri daban daban, a kuma karkashin wannan yanayi, tunanin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar game da "kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya", wato kasar Sin tana fatan daukacin kasashen duniya za su samu ci gaba tare, tunani ne dake nuna cewa, kasar Sin tana da hangen nesa wajen kiyaye moriyar dan Adam. Kuma ana iya cewa, tunanin yana da muhimmanci matuka ga ci gaban kasashen duniya, tare kuma da ci gaban MDD baki daya.

A ranar 10 ga wata, kwamitin raya zamantakewar al'umma na MDD, ya zartas da wani kuduri game da "yunkurin raya huldar abokantaka da kasashen Afirka", inda aka yi kira ga kasashen duniya, da su kara karfafa goyon bayansu ga ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasashen Afirka, bisa tushen gudanar da hadin gwiwa na cimma moriyar juna, karkashin tunani na kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya. A karon farko an rubuta wannan tunani a cikin kudurin MDD.

Kwamitin raya zamantakewar al'umma na MDD daya ne daga cikin kwamitoci guda tara, wadanda ke karkashin hukumar raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta MDD. Muhimmin aikinsa shi ne yin nazari, da kuma tattaunawa kan yanayin zamantakewar al'ummar da kasashen duniya ke ciki, da makomarsu, kana zai gabatar da shawarwari kan manufofin raya zamantakewar al'umma, da matakan da za a dauka, domin samun kyautatuwa a fannonin matasa, da tsofaffi, da nakasassu, da iyalai da dai sauransu. Ana sa ran gabatar da kudurin kwamitin ga muhimman hukumomin MDD domin tattaunawa.

Shugaban kwamitin Mr. Philip Chaves, ya bayyana cewa, daukacin mambobin kwamitin su 46, sun shiga tattaunawa kan daftarin kudurin, wanda ya samu goyon baya daga rukunin kasashe 77. Chaves ya kara da cewa, yayin da ake tattaunawa kan daftarin, an amince da tunanin "kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya". A ganin sa, ba za a iya yin watsi da wannan tunani a yayin taron MDD ba.

A ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2017, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron shugabanni mai taken "kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya", taron da ya gudana a fadar "Palace of Nations" dake birnin Geneva, inda ya bayar da wani jawabi, wanda ya shafi wannan tunanin daga duk fannoni. Yanzu dai an rubuta tunanin cikin kudurin MDD, wanda hakan ke nuna cewa, tunanin ya riga ya samu karbuwa a wajen yawancin kasashe mambobin MDD, wanda hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa, wajen gudanar da harkokin duniya yadda ya kamata.

Har wa yau wannan tunani ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna kara dogaro da juna, kasashe manya masu karfi, da kanana masu fama da talauci, babu banbanci, wajen dogaro da juna. Alal misali, ana iya ganin hakan daga tasirin da 'yan gudun hijirar da suka tsira daga kasashen yammacin Asiya da na arewacin Afirka sakamakon yake-yake ke kawo wa kasashen Turai. Hakika idan wasu al'ummomi a duniya suna jin dadi, yayin da wasu ke fama da matsaloli, to, hakan ya sabawa makomar da MDD ke sa ran cimmawa.

Shugaban kwamitin Chaves ya ci gaba da cewa, tunanin "kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya" ya sa kaimi ga kasashen duniya, da su samu ci gaba ta hanyar kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, kuma hakan ya dace da ka'idar MDD. Bugu da kari a bayyane ta ke cewa, wannan tunani yana da muhimmanci ga MDD, yayin da take kokarin cimma burin samun dauwamammen ci gaba a fadin duniya. Chaves ya ce, idan ana son cimma wannan buri, baya ga bukatar kasashe daban daban a fadin duniya su yi kokarin raya tattalin arzikin su a cikin gida, a hannu guda ana bukatar kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za a gudanar da harkokin kasashen duniya lami lafiya. Idan kasashen duniya suka ki gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, to, kuwa ba zai yiwu a tabbatar da burin samun dauwamammen ci gaba ba.

Yanzu dai kasashen duniya na kara gano cewa, al'ummomin fadin duniya suna rayuwa ne a doron duniya guda daya, don haka suke da makoma guda daya. A saboda haka, kasar Sin da kawancen kasashen Turai, da kasar Amurka, suka zartas da yarjejeniyar Paris game da tunkarar matsalar sauyin yanayi a watan Disambar shekarar 2015.

Chaves ya kara da cewa, idan an yi la'akari da moriyar al'ummomin kasashen duniya cikin dogon lokaci, tabbas za a ga cewa, kasashen duniya da MDD, za su samu moriya daga wannan tunani, duba da cewa wannan tunani na kunshe da bukatar yin hangen nesa, ta yadda ba za a mai da hankali kan moriya dake gabansu kadai ba. Ya ce, kasar Sin tana da dogon tarihi, shi ya sa Sinawa ke da hangen nesa. Ana iya cewa, tunanin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar game da "kafa wata duniyar dan Adam mai makoma guda daya" ya gaskata cewa, al'ummun kasar Sin suna da hangen nesa wajen kiyaye moriyar dan Adam, musamman ma moriyar dan Adam cikin dogon lokaci. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China