Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Guangzhou Evergrande ta zama zakara a gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Asiya AFC a shekarar 2013, gasar wasan kwallon kafa ta Sin wato CSL ya kara samun ci gaba a shekarun baya, yanayin wasan kwallon kafa da kasar Sin ke ciki ya jawo hankalin jama'a da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Amma duk da irin bunkasuwa da aka samu, kamata ya yi a mayar da hankali wajen horar da yara kwallon kafa a kasar Sin, hakan zai sa kasar ta bunkasa a fannin kwallon kafa. A yanzu haka, ra'ayin jama'a shi ne na samun horo a kasashen ketare a fannin wasan kwallon kafa. A cikin wadanda ke samun horo a ketare, akwai wata kungiyar wasan kwallon kafa ta musamman, mai kunshe da 'yan mata masu shekarun haihuwa 17 zuwa 18. A cikin shirinmmu na yau za mu kawo muku bayani game da wannan kungiyar.
170220-Kungiyar-wasan-kwallon-kafa-ta-mata-dake-samun-horo-a-kasar-Brazil-Bilkisu.m4a
|