170213-Kasar-Sin-na-kokarin-kyautata-manufar-haihuwa-yaya-biyu-Kande.m4a
|
Ranar daya ga watan Junairun shekarar 2016 ya kasance rana mai matukar muhimmanci, domin baya ga bikin sabuwar shekara, wata ranar ce kuma da gwamnati ta sauya tsarinta na kayyade iyali wanda aka riga aka aiwatar da shi har fiye da tsawon shekaru 30, inda ta ba ma'aurata zabin haihuwar 'yaya biyu, al'amarin da ya kuma bada damar samun dorewar yawan adadin al'ummar kasar.Ya zuwa yanzu dai, an riga an aiwatar da tsarin har fiye da tsawon shekara guda,yaya tasirin tsarin? Kuma ta wadannen fannoni ne kasar Sin ke kokarin kyautata tsarin? Bari mu saurari shirinmu na yau tare.(Kande Gao)