in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin murnar ranar rediyo ta duniya a Shanghai
2017-02-14 10:42:58 cri

Jiya Litinin 13 ga watan Fabrairu, ita ce ranar rediyo ta duniya karo na shida da hukumar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'ada ta MDD UNESCO ta kebe, an kuma gudanar da biki a birnin Shanghai na kasar Sin domin murnar wannan ranar, wanda shi ne karo na farko da aka shirya irin wannan biki a yankin Asiya.

A shekarar 2011, hukumar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'ada ta MDD UNESCO ta kebe ranar 13 ga watan Fabrairun ko wace shekara a matsayin ranar rediyo ta duniya, a wannan rana, al'ummomin kasashen duniya su kan shirya bukukuwa iri daban daban domin murnar wannan rana, tare kuma da nuna fatan alheri ga ci gaban da rediyo ya samar a fannin yada bayanai da al'adu tsakanin kasashen duniya. Jiya ne ranar rediyo ta duniya karo na shida da aka kebe, domin murnar wannan ranar, an kuma gudanar da biki a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda kuma shi ne karo na farko da aka gudanar da wannan biki a yankin Asiya.

A halin da ake ciki yanzu, kafofin watsa labarai a fadin duniya, musamman rediyo suna fuskantar manyan sauye-sauye sakamakon ci gaban yanar gizo, haka kuma sun samu damammaki da dama da ba su taba samu ba a baya.

Mataimakin shugaban babbar hukumar kula da harkokin rediyo da fina-finai da telebijin ta kasar Sin wato SARFT Tong Gang ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan ci gaban da rediyo ya samar, kuma ta bullo da tsarin watsa labarai da ya amfani al'ummar kasa mafi yawa a fadin duniya, adadin da ya kai kaso 99 bisa dari a kasar Sin, kana ta bullo da tsarin watsa labarai domin biya bukatun gaggawa, Tong Gang ya ci gaba da cewa, a karkashin irin wannan sabon muhalli, kafofin watsa labarai na kasar Sin suna kokarin yin kwaskwarima domin kara samun bunkasuwa. Tong Gang yana mai cewa, "Bisa bunkasuwar fasahohin zamani da fasahohin yanar gizo, aikin watsa labarai ya samu ci gaba cikin sauri, wanda ya kasance a kan gaba wajen saurin isar da bayanai, da tattaunawa da juna tsakanin masu sauraro ko masu karanta labarai, kana domin kara biya bukatun jama'a, kafofin watsa labarai na kasar Sin suna kokari matuka domin samar da hidima a dukkan fannoni, ba ma kawai suna kokarin watsa labarai ga masu sauraro ba, har ma suna kokarin kirkira abubuwan da za su kara jawo hankalin masu sauraro."

Kawo yanzu an samu babban ci gaba a fannin hanyoyin watsa labarai sakamakon bunkasuwar fasahohin yanar gizo, babban sakataren kawancen watsa labarai na Asiya da tekun Pasifik Javad Mottaghi ya bayyana cewa, dandalin cudanyar jama'a game da yanar gizo ya samar da wani dandali mai kuzari ga watsa labarai, yana mai cewa, "Baya ga watsa labarai, ana kuma samar da kide-kide da wake-wake a dandalin cudanyar jama'a ta yanar gizo, kana kafofin watsa labarai ta yanar gizo a fadin duniya suna karuwa cikin sauri, ana iya cewa, ana watsa labarai ta sabuwar hanyar yanar gizo."

Yanzu kafofin watsa labarai na kasar Sin suna kara mai da hankali kan labaran da suke watsawa ga masu sauraro, kuma suna kokarin kirkiro wasu abubuwa domin kara kyautata hanyoyin watsa labarai, a sa'i daya kuma, suna ba da muhimmanci kan cudanyar dake tsakanin su da takwarorinsu a fadin duniya, ta yadda za su koyi fasahohi daga wajen su, tare kuma da samun sabbin hanyoyin watsa labarai masu tsarin musamman na kasar Sin a dandalin kasa da kasa.

Kawo yanzu, gidan rediyo da telebijin dake birnin Shanghai na kasar Sin ya bullo da sabbin manufofi domin raya aikinsa, shugabar gidan, kana shugabar rukunin raya al'adu da rediyo da fina-finai da telebijin na birnin Shanghai Wang Jianjun ta yi mana bayani cewa, ya zama wajibi a hada aikin watsa labarai da yanar gizo, kuma birnin Shanghai ya riga ya samu sakamako mai faranta ran mutane a fannin karfafa cudanya tsakanin kafofin watsa labarai daban daban na birnin, Wang Jianjun ta bayyana cewa, "Mun kafa cibiyar watsa labarai ta Dongfang ne ta hanyar hada wasu sassan watsa labarai guda 13, kana muna amfani da sabuwar fasaha wajen watsa labarai, muna kuma amfani da kwarewarmu domin kara samar da bayanai ga masu sauraro ta hanyar yanar gizo, ana iya sauraron shirye-shiryenmu ta hanyar yanar gizo. Wannan ya nuna cewa, mun samar da wani dandali kuma, kawo yanzu gidajen watsa labarai a fadin kasar sama da 90 sun shiga wannan dandali."

Taken ranar rediyo ta duniya na bana shi ne "Aikin watsa labarai ya shafi kowa da kowa." Babban jami'in UNESCO Frank La Rue ya ce, aikin watsa labarai zai samu ci gaba cikin sauri, idan har kowa da kowa ya ba da gudummawar da ta dace. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China