in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Afirka ta Kudu na kokarin kyautata tsarin tattalin arziki da zaman takewar al'ummarta
2017-02-13 10:35:03 cri

A ranar 9 ga watan nan da muke ciki ne, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya gabatarwa taron majalisar wakilan al'ummar kasa wani rahoto game da yanayin da kasarsa ke ciki a shekarar 2017, inda ya jaddada cewa, gwamnatinsa za ta yi kokari matuka domin kyautata tsarin tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasar. Ana ganin cewa, rahoton zai yi tasiri ga makomar tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar ta Afirka ta Kudu a cikin 'yan shekaru masu zuwa, wata kila ma zai yi tasiri ga kasar baki daya a cikin shekaru sama da goma masu zuwa.

A baya, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya taba ambato batun kyautata tsarin tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar, kuma yanzu ya sake tabo lamarin, inda ya yi cikakken bayani a kan batun, hakan ya nuna cewa, shugaba Zuma ya kara mai da hankali kan lamarin.

A shekarar 1981, fitaccen jagoran yaki da wariyar launin fata na Afirka ta Kudu Oliver Tambo ya taba gabatar da wani jawabi game da manufofin gina kasa a yayin taron shekara shekara na jam'iyyar kwaminis ta Afirka ta Kudu, inda ya bayyana cewa, makasudin yin gwagwarmayya a Afirka ta Kudu shi ne domin tabbatar da ka'idojin 'yancin kai wadanda ke kumshe da manufar 'yantar da tattalin arziki a kasar, to, idan ana son cimma wannan burin, wajibi ne a mayar da dukiyar kasa ga hannun al'ummar kasa, kana idan ba a warware matsalolin da ake fuskanta ba, ba zai yiyu a tabbatar da adalci a kasar ba, a saboda haka dole ne a 'yantar da tattalin arziki a kasar ta Afirka ta Kudu.

Amma tsohon shugaban jam'iyyar ANC Tambo bai cimma nasara kamar yadda yake so kafin ya riga mu gidan gaskiya ba, daga baya mutumin da ya maye gurbinsa marigayi Nelson Mandela ya gabatar da manufar sulhuntawa tsakanin kabilun kasar, hakan ya kare moriyar fararen fata a fannin tattalin arziki. Yanzu dai shugaban kasar Afirka ta Kudu mai ci Zuma ya sake bullo da burin Tambo, kuma ya yi bayani kan manufofinsa game da sauya tsarin tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar, dalilin da ya sa haka shi ne domin yana ganin cewa, daukacin al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu za su amfana da wannan tsari, musamman ma matalauta da mata wadanda adadinsu ya fi yawa a kasar.

Shugaba Zuma zai dauki matakin ne bisa dalilin babbar gibin dake tsakanin kudin shiga na iyalan bakaken fata da fararen fata, yanzu a ko wace shekara, adadin kudin shiga na ko wane iyalin fararen fata ya zarta na iyalin bakaken fata a kalla sau biyar. Kana a birnin Johnnesburg, a cikin manyan kamfanoni dari daya, goma ne kawai suke karkashin mallakar bakaken fata, ban da haka kuma, duk da cewa, adadin fararen fata a kasar ta Afirka ta Kudu bai kai kaso 10 bisa dari a cikin daukacin al'ummar kasar ba, amma adadin manajojin dake aiki a kamfanonin kasar ya kai kaso 72 bisa dari, shugaba Zuma yana ganin cewa, idan ba a kawar da wariyar launin fata a kasarsa ba, to, ba zai yiyu ba a samu ci gaban tattalin arziki.

Shugaba Zuma ya bayyana cewa, tun daga yau gwamnatin Afirka ta Kudu za ta fara daukar matakai domin kyautata tsarin tattalin arziki da zaman takewar al'umma, Zuma ya ci gaba da cewa, domin tabbatar da nasarar aikin yadda ya kamata, gwamnatin kasar za ta dauki matakai a fannoni daban daban, misali kafa dokoki, da ba da izni ga kafa kamfanoni, da tsara kasafin kudin kasa, da kuma kara samar da damammaki ga bakaken fata ta yadda za su kara kokari wajen gina tattalin arzikin kasa, wannan zai taimaka wajen ciyar da tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu yadda ya kamata.

Kazalika, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu za ta kara mai da hankali kan kwaskwarimar da ta ke aiwatarwa a fannin gonaki, da kyautata sharadin gidajen kwana, da kuma zuba jari, alal misali, sake rarraba gonaki ga al'ummar kasar domin kara kyautata yanayin da manoman kasar ke ciki.

Idan aka yi la'akari da rahoton da shugaba Zuma ya gabatar, ana iya gano cewa, gwamnatin Afirka ta Kudu tana gudanar da kwaskwarimar tsarin tattalin arziki ne ta hanyar kafa dokoki, kuma bisa matakai daban daban, ta sa niyya mai karfi, amma tana aiwatar da matakan ne bisa doka. Duk da cewa, akwai 'yancin kai da tsarin dimokuradiyya a kasar ta Afirka ta Kudu tun kusan shekaru 22 da suka gabata, amma har yanzu yawancin bakaken fata ba su da wadata, kuma sun nuna rashin dadi kan yanayin da suke ciki. A saboda haka, za a dauki lokaci, idan har ana son warware matsalolin da kasar ke fuskanta a cikin shekaru sama da 20 da suka gabata. Sannan dole ne shugaban kasar ya kara yin hakuri, kwazo da kuma hangen nesa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China