in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar WCO: ana yin hadin gwiwa sosai da kasar Sin wajen bunkasa tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban
2017-02-09 11:26:00 cri


A kwanan baya, a lokacin da babban sakataren kungiyar kwastam ta kasa da kasa WCO Mr. Kunio Mikuriya ke ganawa da wakiliyarmu a birnin Brussels, ya bayyana cewa, jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a yayin taron tattaunawa na Davos a watan Janairu, ya kawo wa jama'a kuzari. Ya ce jawabin ya mika sako muhimmi game da yadda kasar Sin, wadda ta kasance tamkar wata kungiyar tattalin arziki mafi girma ta biyu a duk fadin duniya ke nuna goyon baya ga tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban.

Hukumomin kwastam na kasar Sin ma a kullum suna yin hadin gwiwa sosai da kungiyar WCO, wajen ci gaban tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban.

Kungiyar kwastam ta kasa da kasa WCO, ita ce kungiyar kasa ta kasa daya tak da gwamnatocin kasa da kasa suka kafa, domin nazarin harkokin kwastam. Babban sakataren kungiyar Mr. Kunio Mikuriya, ya gaya wa wakiliyarmu cewa, nauyin farko dake wuyan kungiyar shi ne ingiza bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa. Ya ce a lokacin da ake shirya taron tattaunawa na Davos a watan Janairu na bana, ya saurari jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar. Mr. Kunio Mikuriya ya ce, wannan jawabi ya burge duk wanda ya saurara a yayin taro.

"Ba ni kawai ba, jawabin ya burge duk wanda yake dakin taron, sabo da a bayyane yake Xi Jinping na goyon baya ga kokarin bunkasa cinikayya tsakanin sassa daban daban. Ko shakka babu, kasar Sin ta riga ta ci gajiya, sauran kasashe ko yankuna ma suna cin gajiya daga wannan tsari na cinikayya tsakanin sassa daban daban. An sa mini kaimi, sabo da wata babbar kungiyar tattalin arziki ta ce za ta nuna goyon baya ga tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban, wannan wani muhimmin albishiri ne."

Kunio Mikuriya yana ganin cewa, a kullum kasar Sin na kokarin ingiza bunkasa tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban. Kungiyar WCO ita ma na kara yin hadin gwiwa sosai da hukumar kwastam ta kasar Sin. Ya kara da cewa, "Alal misali, a wajen bunkasa cinikayya ta shafin intanet, wato E-Commerce a Turance, kasar Sin ce ke shugabantar wannan sashe wanda ke karkashin jagorancin WCO, kuma tana kokarin sanya mutane su shiga cinikayya ta shafin Intanet cikin sauki. Sakamakon haka, ana ganin cewa, kasar Sin na nuna goyon baya sosai ga kungiyar WCO."

A lokacin da ake samun ci gaban fasahohin zamani, yin cinikayya ta shafin intanet yana ta samun karbuwa sosai a duk fadin duniya, wannan ya sa hukumomin kwastam ke fuskantar kalubaloli da yawa. Ko da yake kawo yanzu kungiyar WCO ta riga ta fitar da wasu ma'aunoni da ka'idojin kula da harkokin cinikayya ta shafin intanet, amma ba su iya isa saurin bunkasuwar cinikayya ta shafin intanet. Sakamakon haka, kungiyar WCO ta kafa wani sashen aiki dake kula da harkokin cinikayya ta shafin intanet, wanda yake nazari kan yadda za a iya buga harajin kwastam kan kayayyaki masu rahusa, da tabbatar da ganin ko ana saye ko sayar da abubuwan dake cikin karamin kunshi bisa doka ko a'a, da kuma yaya masu yin cinikayya ta shafin intanet za su iya daidaita bayanan da ya kamata a rubuta a jikin kunshi, da sauran jerin matsaloli iri iri, kuma zai fitar da wasu sabbin ka'idodi.

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta kuma yi nazari kan batun yin cinikayya tsakanin kasa da kasa ta shafin intanet, har ma ta bayar da wasu shawarwari masu dacewa ga kungiyar WCO.

Mr. Kunio Mikuriya ya kuma bayyana cewa, yanzu haka kasar Sin tana ganin cewa, ana fuskantar kalubale sosai wajen bunkasa tattalin arziki na bai daya a duk fadin duniya, tana kuma maida hankali sosai wajen tabbatar da ganin an yi cinikayya tsakanin kasa da kasa lami lafiya. Mr. Kunio Mikuriya yana mai cewa, "Kasar Sin ma tana sane da cewa, kokarin bunkasa tattalin arziki na bai daya tsakanin kasa da kasa ba shi da ginshiki mai karfi. Sabo da haka, a yayin taron G20 da aka shirya a birnin Hangzhou na kasar Sin a bara, shugaba Xi Jinping ya gayyaci kungiyar WCO, da ta zama daya daga cikin mambobi kungiyoyin kasa da kasa, wadanda suke kokarin dakile laifin zamba a fannin hada-hadar kudi."

A cikin "sanarwar taron kolin G20 na Hangzhou" da aka zartas da ita a bara, akwai wani babi, inda aka nuna cewa, "a lokacin da ake yin cinikayya tsakanin kasa da kasa, idan an samu rasiti mai kunshe da kuskure na ganganci, hakan zai zama laifi na musayar kudi, wanda zai kawo illa ga kasa da kasa a bangaren hada-hadar kudi bisa burin neman ci gaba. Za mu ci gaba da dakile irin wannan laifi. Muna kuma fatan bangarori daban daban za su yi hadin gwiwa da kungiyar WCO, domin nazarin rahotannin da abin ya shafa bayan taron kolin G20 na Hangzhou." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China